kuma ta dawo 'Yar Gudulle wato Gudaliyarsa kenan.....
muje zuwa fans wannan na Musamman ne Kuma na Dabanne acikin Buks dina zaku nishadantu zaku fadakantu Sai naga comment dinku.
luv you all my fans💋
[5/5, 21:41] Hayat: *'YAR GUDULLEN SARKI* 🏹🤾♀️🏇
(Labarin Cakwakiyar Masarauta)
*Nabilancy Luv* 💘(Auntyn S & S)
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-associationz
*_________________________________*
Page -2️⃣
Fulani Zinaru na shiga sashin mai Martaba ta canza fuska so take ya fahimci Ranta abace yake tunda tagama gano lagonsa baya kaunar yaga rashin fara'arta ko yaganta atashin hankali tun tali tali haka suke zamansu dama kowa na gudun bacin ran kowa wannan shine zama na Amana da gaskiya da kaunar juna.
ba kamar yanda Amarya Iyami ke nuna halin ko inkula dashiba ita babu ruwanta da sabgarsa tata kawai takeyi bata fiya bashi kulawa ba ita dai barta da izza da mulkin ita matar sarki ce dole abita aduk inda take shikuma tana nuna masa girman kai sbd tana takamar ita diyar me kudi ce bazata kaskantar da kantaba,takan manta miji shine asama da matarsa kuma shi sarki a duk inda yake sarki ne,ko ita Fulani da take da gadon sarauta bata nuna hali irin na Amarya iyami.
zamansu dai da juna saffa saffa babu rikici me yawa sbd yanda fulani ta rike girmanta bata fiya shiga sabgar ta ba.
dama iyamin ke nuna kishi da fulanin amma Sam fulani zinarun ma bata biye mata ayi.
Kallon fuskar fulani kawai mai martaba yyi yasha jinin jikinsa ba lafiya ba
a yanayin zaman da tayi ma bata ko kalli inda yake ba ta miko masa gaisuwa fuska ba fara,a yasan akwai magana.
gabansa saida ya fadi amma sai bai nuna mata ya fahimta ba kada ya jangwalo wani abun shidai tunaninsa yabashi ko akan maganarsu da itane na Fitar da jiddah daga gidan.
Andau tsahon mintina kana ta magantu dan kanta sbd shi Carbi ne ahannunsa yana ja yana tasbihi abinsa baice mata komai ba.
"Magana nazo da ita akan Yarinyar nan jiddah daka canzawa suna takoma gudullenk akan wani dalilin kayi hakan,kana so kanunawa duniya kana kaunar ta ne ko Yaya,?ashe har samun damar zama da ita kakeyi na wasu lokutan ban saniba.,?
murmushin dattawa na dabanne, daya murmusa saida cikar zatinsa ta karu ita kanta zuba masa idanu tayi tana kallonsa ganin yanda ya canza mata yau dayai wannan murmushin sai taga kamar danta yarima ne agabanta,tabbas ana cewa suna kama saiyau takara tabbatarwa kanta.
A hankali Takawa ya furta"Wato fulani na fahimci so kike ki koyi zafin kishi na wasu matan marasa sanin ciwon kansu ko?
ta sadda kanta kasa ji tayi kamar kasa ta bude ta shige dan kunyar sa da taji wannan kalamin nasa ya daureta dayawa.
Yaci gaba da cewa"Abinda na fahimta zuwan yarinyar nan yana so ya canza kyawawan halayenki na Arziki haba me Babban suna,ina hankalinki yake? ni ayanzun da kika ganni murna nake na samu diya mace agabana da nake da muradin samunta tuntuni,kinfi kowa sanin yanda nake kaunar naga inada 'ya mace amma Allah bai bani ba,walh a yanxun haka bana yiwa yarinyar nan kallon matar Aure na sai 'yar cikina,Amana kuma take agurina atunani na fa nayi tsammanin zaki tayani rikon Amanar nan,kuma azahiri kina nuna mata kaunar zama da ita da hakan yasa itama ta saki jiki dake umman ta,sai gashi a bayan idonta kina nuna fuska biyu,nafiso kitsaya aguri daya ki nuna mata kauna ta fisabilillahi ko kya shiga Aljanna salin alin babu zunubinta akanki,ki daure ki cije kamar yanda nasanki tun afarko da dauriya akan kishi.....tayi saurin dakatar dashi "walh ni ba kishinta fa nakeyi ba akwai babban dalilin dayasa nake hakan.
yace"to meye dalilin da baza'a iya gayamin ba,nifa babban masoyin ki ne,abokin shawararki uban yaronki kuma dan,uwa agunki haba uwar gidana me halin kwarai bana jin dadin yanda kika birkice min akwana biyun nan fa.
har ga Allah tanajin dadin yabon da yake mata ita anan ma yake samo lagonta don duk yanda takejin zafin abu daya kalailayeta shikenan take hkr ta saki.
murmushi tayi tace"to nidai ko ma meye abar wannan batu kuma kasa aranka nima bana kishi da 'yar gudullen taka.
Shima murmushin yayi yace"Inama kema zaki dawo fada mata wannan suna da naji dadin hakan da kin kara faranta min sosai matata.
Tace"ikon Allah wai to meye dalilin wannan sunan,?
ya gyara zama yace"Badda bami nakeso nayiwa jama'a inaso kowa yasan ina son Jiddah agidannan amtsayin 'ya.inaso itama tasan a matsayin 'ya nake kallonta wannan shine dabarata kuma nasaka gobe idan an sauko sallar juma,a ayi shelar sunan jiddah ya dawo 'Yar gudullen sarki, wato gudaliyata da nake jinta araina daya tilo agareni.
murmushi tasakeyi tace"Lallai kana so ka haifar da wani kishin anan gaba kashi biyu.
Da mamaki yace mata"Kamar yaya kashi biyu,?to da ina da ina?
itama gyara zaman tayi tace"na farko kasan matarka Iyami tana da tsananin kishi zata iya tsangwamar 'yar taka.sannan kuma yarima idan yadawo yatarar ka canza soyayyar da kake masa da ta gudaliyar taka to tabbas bazaiji dadi ba tunda a yanda ka daukaki abin sai ayi zaton baka da d'a ko 'ya ne aduniya sai ita kawai.
girgiza kai yahauyi yana fadin"wannan ba dalili bane dole zaiyi uzuri idan ya fahimta nasan yana da hankali bare yanzun yakaro hankali da ilimin zaman takewa haka zalika yarima me tausayi ne idan yadawo yaji batun gudullena na maraici natabbata zai tausaya mata.
Tahau gyada kai tana fadin"Haka ne na yarda da batunka amma matarka fa,?
yace"to ai ita ba komai bace akan sabgar gidana tunda bata nuna kulawarta akaina da soyayyarta akaina sai sarautar kawai take so da arzikin gidan duk rufin asirin iyayenta amma tana hangen wani tamkar bata taso cikin arzikin ba,kuma indai tace zata takurawa gudullena to tabbas nima saina takura mata don bazan dauka ba.
Fulani tace"hhhuum Maganar karatun da nakeso atura gudullen taka nakeson jin ina aka kwana,ka gama yanke shawarar ne ko yaya,? saboda munyi magana da yarinya ta nuna tana son tayi dogon karatu arayuwarta kuma kasar da yarima yake takeso.
Kura mata ido yayi kana yaja ajiyar zcy sannan yace"wannan nasan duk shirin kine kuma ban amince ba,idan ina bin abinda kikeso nima dole kibi abinda nakeso nima,na gama kansile maganar babu inda gudullena zataje so nake na jajirce na tsaya tsayin daka naga ta sami tarbiyya agaba,inyaso idan ta girma takai munzali sai in sahale mata Auren kaina inbata wanda takeso inta fito dashi amma yin nesanta damu za.a iya samun matsala arayuwarta kuma Allah mu zai tambaya akan tarbiyyarta kuma kema kinsan da hakan dan haka dan Allah fulani kibar maganar nan kitayani renonta kafin girmanta.
Fulani tace"to naji na kuma yarda na bar zancen saidai inaso ka kara gaskata min kalmar daka faranta min rai da ita har zcyrka ka fada kuwa ko kawai ka fadane dan inji dadi zaka sahale mata Auren naka agaba kayi Alqawari,?
ya gyada mata kai yana fadin "Nayi Alqawari duk rintsi duk tsanani bazan karyaba.
tace"To Alhamdulillah nikuma insha Allahu zan yar da komai intayaka renon yr rikon taka zan dage wajen baiwa Yar gudullen taka tarbiyya kamar yanda ka roka.
yace"to nagode Allah yatayamu riko yabamu ikon cika Alqawarin.
Tace "Amin.
*********
Kamar yanda Takawa ya fada ya kuma Rattabawa jama,arsa cewar ayi sanarwar jiddah ta dawo 'yar gudullensa haka kuwa akayi ana idar da sallar Juma,a akai shela akan canjin sunanta.
kuma a yammacin aka tashi mutum uku cikin fadawa suka shishshiga lungu da saqo na cikin gari cewar Jiddah 'Yar sarki dayake riko diyar Dan'uwansa anyi mata canjin suna ta dawo 'Yar GUDULLEN SARKI kamar yanda sarki ya biɗa aringa gaya mata saboda soyayyarsa gareta da matsayin 'yar cikinsa da tadawo.
haka kuwa lamarin ya juye akoina zancen kenan har wasu suna ganin zata iya kwace soyayyar da sarki kewa D'ansa yarima.
A cikin gidan sarki kuwa a bangaren Amarya Iyami wannan abu bai mata dadi ba don tayi fassara akan hakan kala kala.
har bore taje yiwa sarki akan ta kansile wannan sunan.
baice mata uffan ba kam saida tagama maganganunta da koke kokenta akan ita yarinyar nan batayi mata ba.
ya jinjina kansa yace"nikuma yarinyar tafi gaban kowa agidan nan akanta zan iya yiwa mutum komai,Yar gudullena daya take tamkar da dubu wanda duk keson bacin ransa to yaringa tabo ta yagani.
tayi kwafa tace "kana nufin kenan daga zuwanta gidan tafini matsayi kake nufi,kawai naga alamar dan ban taba haihuwa ba shiyasa ban isa komai agun ka ba to walh na fada na kara na tsani yarinyar nan.
ya dago a fusace yai mata kallon banza.
ta tashi da jan ido ta fuce fuuuu
tayi sashinta ranta na mata quna.
daga can nesa Jakadiyarta ta hangota aiko da sauri ta nufi bangaren uwar dakin nata don jin meya fusata ta haka a wannan lokaci data san yau ita ke da sarki amma alamu na nuna ansamu saɓani.
Tana zuwa ta tarar da ita ta zabga tagumi tana ta goge hawaye.
gurfana tayi agabanta tana zuba mata banbadanci da rarrashin ta "ranki ya dade hankalina yatashi ganin yanayinki awannan hali,Allah ya huci zcyrki uwar dakina kiyi hkr ki kwantar da hankalinki kinsan dai kinada hawan jini banason damuwarki ko kadan daure ki gayamin meya faru dake wala Allah insamo mana mafita uwar dakina.
ajiyar zcy taja tace"jakadiya Takawa baya darajtani akan yarinyar can komai ya fito bakinsa gaya min yake sbd bantaba haihuwa ba walh da ace kudi na siyen haihuwa da tuni na tara yara agidannan da ba,ai min cin fuska akan wata shegiyar yarinyar karereba.
jakadiya tayi saurin dora hannunta aka kirjinta na firgici tace"badai 'Yar gudullen sarki ba.
cikin jin haushin sunan dai tace mata"ita mana, walh jakadiya na tsaneta sosai ba da wasa ba zan iya salwantar da rayuwarta walh sbd naga zata iya zamemin masifa agidan nan akanta sarki zai iya sakina nasan da hakan ya kuma nunamin azahiri nagani.dan haka kibani mafita jakadiya inba haka ba zan iya hadiyar zcy inmutu akan yarinyar nan.
jakadiya taja ajiyar zcy tace"wannan abune me sauqi kwantar da hankalinki uwar dakina akwai mafita akusa ma kuwa muda muke da bokanya GOGAL muke da Malam Buba me gani har hanji haba uwar dakina kinsan fa komai kikeso ayi miki akanta zasui miki akan lokaci kalilan.
ajiyar zcy taja tace"naji jakadiya,yaushe yakamata muje gurinsu dukan ayi min maganinta dan rubdugu nakeso ayi a aikin agigita ta fice agarin gabaki daya.
jakadiya tayi dariyar mugunta wawulanta ya bayyana tace"Ai ko ayanzun kikace aje a shirye nake uwar dakina.
Amarya iyami ta gyara zama tace"Hhuumm mubari gobe mufita yanzun bani da damar zuwa tambayar fita gun takawa sai ya huce.
*******
adaren iyami na so taje ta sami mai martaba kan tana son fita amma batasami damar nan ba sbd tana shiga take tarar dashi shida 'Yar gudullen tasa yana mata hira ta ba dariya ita kuwa tana ta kyalkyalawa
sau biyu taje adaren amma bata sami damar zama dashi ba tana shiga yake hade rai haka zalika gudaliya ko kallonta batayi canza fuska ma takeyi kamar zatayi kuka gashi takawa yaqi cewa ta fita
hakan yasa a zuwanta na karshe data gaji da zama ta tashi fuuu tafuce afusace.
shikuwa ko ajikinsa dan dama ba wai ta saba bashi kulawa tayi ba bare ya damu shikuma aduk lokacin dayake zaune yana hira da yar gudullensa yana cikin nishadi baya son tsahirtawa.
ko Fulani ayanxun intashigo ta tararsu suna hira da yar tashi tayasu takeyi in tatsuniya yake mata itama tsoma baki takeyi ayi da ita,ta fahimci yin hakan ne kadai ke faranta ransa shiyasa ta zubda makaman.
Sarki nayiwa Yar gudullensa wani azababben so wanda ko yarima baijin yatabayiwa hakan amma duk wannan abu dayakeji akanta bawai son sha'awa ko dan da auransa akanta ba bane Aa yanayine kawai sbd sabo da haduwar jini kuma yanayi matakallon 'yar cikinsa.
A cikin satin yarima kuma yayo wayar cewar zai zo gida hutu zaiyi wata guda idan yazo din, wanda idan yakoma ne zasu gama karatun duka yadawo gida.
aiko gida yadau murna duk iyayen nasa suka shiga shirye shiryen Zuwan d'an nasu
Yar Gudullen sarki tafi kowa zakwadi da murna mafarkin yayan nata dama takeyi kullum.
burinta akullum dama ace Yaya yarimanta zai dawo.
dayake kusan kullum sai Ummanta ta hadasu awaya sunsha hira tayi ta masa surutai na son zuwa kasar dayake itama tayi karatu ko taita bashi labarin kawayenta data baro na garinsu shidai biye mata kawai yake sbd surutunta dayanda take nuna tana son ganinshi ke burgeshi yanajin dadin hakan.
sunyi sabo ta waya gashi tasanshi a hoto amma shikam bai san fuskar kanwar tashi ba
acan bangaren nashi shima yana dokin dawowar tashi kasar don Ganin sabuwar kanwar tasa wato 'yar Gudullen Sarki.
muje zuwa.....
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group
WHATSAPP NO:+2349030159301
Downloaded from GNOVELS.COM.NG
This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/gnovels
Twitter : https://twitter.com/gnovels
Telegram : https://t.me/gnovels
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels