Share this page
4 / 8
na san ya yi daɗi. Ko da muka gama ɗaki muka shiga muka yi sallah kafin muka dawo falo muka zauna. Can aka fara buga kofar falon kiran mai aiki na yi na ce"Ke buɗe kofar nan" bayan dan lokaci sai ta daow ɗauke da wata leda mai kyau ta ce"Cewa aka yi na Hajiya Sumayya ne" cike da wani irin zafin nama na amshi ledar na ce"Mene ne ki ka tsaya min kikam a ka, wuce ki bani waje" Ledar na shiga buɗe wa nan fa idona ya fito fili kamar za su faɗo kasa tozali da na yi da wasu rantsatun less masu matukar kyau wanda ko ban san kudinsu ba na san suna da tsada. A hankali na fara fito da su ina rafka salati. "Balki taya ni figa uwar miji ta zama kaza, duba ki ga wannan uwar siyayar da aka yi da kuɗin dana, yau Allah na tuba tunda nake ban taɓa saka irin wannan kayan masu uwar tsada har haka ba" na faɗa ina juya less ɗin a hannuna. Balki ta ce"Gaskiya Sa'a kayan sun yi kyau sosai" ɗaya da ciki na ɗauka na miƙa mata na ce"Ga wannan ki dangwali arziki ke ma" hannunta na rawa ta amsa tana cewa"Alhamdulilah, kai Sa'a na gode sosai Allah ya sa ki fi haka Allah ƙara arziki" da amine na amsa. Ni ma na zaɓi guda ɗaya kafin na shiga kiran Sumayya don ta zo ta ɗauki sauran kayanta. ★Sumayya★ Ina daga falona na ji Mama tana kirana da sauri na tashi gabana na dukan uku-uku don har na fara tunanin ko wani laifin na yi mata. Ina isa cikin falon idona suka yi tozali da less ɗin da na yi oder tun wancan watan a wajen Rumaisa. Ga kuma ledar da ke dauke da tambarin shagon Rumaisa din a ajiye a ƙasa. Mama ce ta ce"Zo ɗauki sauran kayanki na zaɓi guda biyu ni ɗaya kawata ɗaya" wani irin bacin rai ne ya taso ya tsaya min a makwoshi sai kuma ta ce"Ko ban isa na dauka ba ne? Ai dai na ga kayan nan kuɗin ɗana ne, kenan ni ma ina da iko a kan su idan ki na da wata magana kuma to sai ki faɗa" girgiza kai na yi na ce"Mama ba ni da abin faɗa" "Ko da na ji ɗauki ledarki ki fice min daga nan" ledar na ɗauka na bar falon. Raina a mutukar bace amman ban ce komai ba na shiga ɗakina tare da ajiye ledar ina bin ta da ido. *Cmnts nd share* [09/12 à 22:07] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 07* Baƙin ciki duk ya ishe ni, babu yadda na iya haka na buɗe sauran less ɗin ina bin su da ido. Ajiye ledar na yi na nufi toilet na yi wanka na canza kayana kafin na sauko ƙasa, yanzu kam Mama ba ta nan da dukan alamu ma kawarta ta tafi. Kitchen na shiga na fara kokarin ɗaura tuwon shinkafa da miyar kuɓewa don tun da Rumaisa ta furta cin abinci da na girka yau kam sai ta ci ko Mustapha ya shiga uku a wajenta. Sai da na gama na jera na su Mama a dinning kafin na haɗa na Rumaisa a cikin babban basket. Na kwashi kayan abincin Qalbi don yau yadda nake jin raina a bace ba zan iya zama tare da su Mama don cin abinci a falon ba. Yadda raina ke min ƙuna na ma rasa me zan yi don jin sauƙin abin da Mama ta yi min. Allah ne shaida ta na ko da na yi order ɗin less ɗin na dauri niyyar na ba Mama Sa'a ɗaya na kaiwa Ummina guda biyu sai na ɗauki guda biyu. Tsaki na ja a cikin raina a fili kuma sai na tashi na shiga wanka domin tsara kwaliyya kafin zuwan Abdallah. Bayan na gama shirin na sauko ƙasa sai ga kiran Rumaisa bayan na ɗaga ta ce"Ke Malama kin yi girkin da rabona?" Kamar tana gabana na gyaɗa kai na ce"Na gama ma madame turo Mustapha ya amsar miki" dariya Rumaisa ta yi ta ce"Ke ma Sumy yo zancen yaushe kuma ai Mustapha ya daɗe da ya ɗauki hanya" dariya na yi na ce"Don Allah Rumy ki rage kwadayin nan haka" "Sai dai ki faɗi duk abin da ki ka ga dama Malama don babu hakurin da zan yi musamman idan abincin gidanki ne" sallama muka yi na kashe wayar. Sai na zauna a falo ina jiran zuwan Mustapha domin yanzu da na tashi na bar falon idan ya zo sai abin ya zama abin faɗi. Da sallama ya shigo falon hannunsa ɗaya riƙe da princesse Aysha ɗayan hannun kuma dauke da kwanukan abinci. Da gudu Aysha ta yi kaina, ɗaga ta sama na yi na rungume ta tsam a kirjina ina sauke ajiyar zuciya don an kai sati uku ban saka ta a idanuna ba ta ce"Momy" cire ta na yi daga jikina ina duba ta sai na ga kamar ta rame sai yanzu na ɗaga kai na kalli Mustapha na ce"Ba ta da lafiya ne?" Girgiza kai ya yi ya ce"Sumayya ina wuni" sai da wata kunya ta kama ni, ba na son ko kaɗan na ji wani abu ya faru da Aysha. Ɗaure wa na yi na ce"Mustapha zauna mana" Waje ya samu ya zauna sai na shiga kitchen na haɗo masa drinks na kawo. Duk inda na saka ƙafa Aysha tana biye da ni, sai da na dauki kwanukan na kai kitchen kafin na dauko ta a hannuna muka dawo falon na zauna na ce"Mustapha ya aiki?" "Alhamdulilah Sumy, Abdallah bai dawo ba har yanzu?" Girgiza kai na yi na ce"Bai ƙaraso ba har yanzu, don Allah Mustapha me yake damun Aysha?" Shiru ya yi kamar ba zai yi magana ba ya ce"Sumy ba na son na ɗaga miki hankali amman maganar gaskiya Aysha ba ta samun kulawar da ta dace a wajen mahaifiyarta" ban yi mamaki ba sanin halin Rumaisa sai na ce"Mustapha ka yi hakuri don Allah, in sha Allah zan same ta na yi mata magana" gyaɗa kai ya yi ya ce"To na gode sosai Sumy Allah ya saka da alkairi" Aysha da ke ta faman kallon cartoon ɗin da na saka mata na zuba wa idanu ina kallonta sai na ji Muryar Mustapha yana cewa "Da a ce ke ce mahaifiyarta da ta ji daɗin rayuwarta don ko ba komai za ta samu kulawa" girgiza kai na yi na ce"Kar ka ce haka Mustapha, ka san sarai halin Rumaisa da an yi mata magana za ta gyara" bai ce komai ba sai can ya ce"Ina Mama?" "Tana ciki, bari na kira ta ku gaisa" ina tashi da niyyar tafiya Aysha ta sauko daga kan sofa ta rike min riga. Jan hannunta na yi muka nufi dakin Mama da sallama na tura kofar ɗakin daƙyar ta amsa min amman ganin Aysha sai ta saki murmushi. "Maraba da mai babban suna, Hajiya Indo ina Mamanki?" Ta faɗa tana miƙa ma Aysha hannu alamar ta zo gare ta. Takawa ta yi har ta ƙarasa bakin gadon nan ta shiga yi mata magana kamar babu ni a wajen. "Mama, Mustapha yana falo yana son ku gaisa" na faɗa ina ɗari-ɗari gudun abin da zai je ya dawo. Ai kuwa ta ce"To baƙar manafuka sai yanzu da ki ka gama ƙare min kallo ki ka tuna da wani Mustapha ko? To je ki ce ina zuwa" miƙa wa Aysha hannu na yi na ce"Zo mu je" Mama ta yi saurin janye Aysha ta ce"Aikin banza idan ki na son ki yi iko da ƴa ki haifi taki kafin ki tsira yin iko da ita don wannan dai da uwarta, kuma abin farin cikin ma duk duniya sun shaida Mustapha bai auri juya ba sai Abdallah da ya yi zaɓen tumun dare ko ɓari ba ki taɓa yi bare kuma a kai ga haifo santala-santalan yara" shiru ban ce komai ba sai juya wa na yi da niyyar barin ɗakin. Ina ƙarasawa cikin falon ya yi daidai da shigowar Abdallah falon. Zuwa ya yi ya rungume ni ya ce"Babe babu oyoyo?" Da sauri na haɗiye kukana na ce"Sannu da zuwa Qalbi" Cikin falon muka ƙarasa sai Mustapha ya ce"Ba shakka ita soyayyar a gaban idonmu ma ba a jin kunya ko?" Da sauri na ɓoye kaina a kirjin Abdallah sai Mustapha ya fashe da dariya ya ce"Aikin banza ki ka yi Sumayya ai kin gama yin rashin kunyar ma" cire ni daga kirjinsa ya yi ya ce"Ke Babe rabu da shi, ina wani rashin kunya ke da mijinki" Zame jikina na yi kafin na tsiyaya drinks a cup na miƙa masa, amsa ya yi ya ce"Tanks you Babe" sai ya zauna suka fara tattaunawa maganar office da Mustapha. Falona na koma ni ma na ci gaba da aikin gabana. Bayan wani lokaci sai ga kiran Rumaisa ina ɗaga wa ta ce"Malama ina mijina?" Ido na zaro cikin wasa na ce"Kar ki ce min bai dawo gida ba har yanzu?" Rumaisa da ke kwance a kan sofa tana jiran zuwan Mustapha don wata irin yunwa take ji kuma ta riga ta ɗaura ran cin abincin Sumy yau ɗinan, ta yi saurin tashi zaune ta ce"Tsakani da Allah Sumy Mustapha ba ya gidanki?" Girgiza kai na yi kamar tana gabana na ce"Da gaske nake yi miki Hajiya Rumy" tashi ta yi ta figi gyalenta da makulin motarta ta ce"wallahi sai Mustapha ya faɗa min wajen yar iskar da ya je, kuma ma tsabar rainin hankali har da ƴata zai tafi hira" Fashe wa na yi da dariya har da riƙe ciki na ce"Allah ya shirye ki Rumy da wannan uban baƙin kishin, Mustapha yana falo tare da Qalbi, bari na je na bashi abinci ya kai miki gimbiya" wata ajiyar zuciya ta sauke wadda har ina iya jiyo sautinta daga cikin wayar. Falon na sauko na tarar su na shan hirarsu na ce"Qalbi ka yi hakuri ka saki mijin wancan matar hakan nan, don wallahi yanzu muka gama waya tana masifa" tsaye Mustapha ya tashi kamar wanda aka tsikara ya ce"Allah na gode maka kin ga fa Abdallah ya rufe ni da surutunsa da ba ya ƙare wa har na manta da sauraniya ce ta aiko ni" dariya na yi na ce"Duk wannan ɓarin jikin na tsoron Rumy ne?" Dariya Abdallah ya yi ya ce"Babe dan Allah bashi abin da aka aiko shi ya amsa. Idan ba haka ba kin san sarai zane shi za a yi" Kitchen ɗin na nufa na ɗauko kayan abincin da na haɗa a basket na kawo mishi Qalbi ne ya ce"Ikon Allah wai dama kai abinci aka aiko amsa" kamar wani maraya Mustapha ya saki tausayi ya ce"Don Allah Abdallah kira min Mama na yi mata sallama na tafi gida" dariya na yi na ce"Kai kam Rumy ta saka ka uku, amman ka bar min princesse yau gobe idan Allah ya kai mu zan kai ta gida" amsa min ya yi da to kafin Mama ta fito suka yi sallama na ja hannun Aysha muka nufi ɗakina har da bye bye take yi wa Daddynta. Bayan Mustapha ya tafi Abdallah ya shigo ɗakin yana dariya na ce"Qalbi ka daina yi mishi dariya fa, don kai ma ba a san ya kake yi idan matarka ta aike ka" girgiza kai ya yi ya ce"To ai ni matata ƴar aljanna ce ba ta yi min irin faɗa da Rumy ke yi wa Mustapha" Ni ma dariya na yi na ce"To kai ina évidence ɗinka a kan Rumy tana yi mishi faɗa, kawai tsoron kar ya ɓata mata rai ne yake yi" murmushi ya yi ya ce"Yau kam na san ba za a bani abinci a baki ba tunda dai ga princesse" "daɗi na da kai Qalbi ka na saurin gane abubuwa" Wanka na yi wa Aysha don dama akwai wasu kayanta a gidan kafin na kwantar da ita tare da yi mata addu'a na dawo falo na tarar da Qalbi na zauna a kusa da shi ina yi mishi hira kamar babu abin da yake damuna. *HAJIYATA KI NA INA NE? AI DAI BA KI MANTA LABARIN tura ta kai bango BA DA KUMA LABARIN Kuskure.* *To zo yau ga labarin DA WATA KUSAN... Wadda bahaushe ke cewa gara nesa.* *Labarin ya fara daukar zafi fa, Hajiya ki biya kudin karatunki kawai sai mu haɗu a Paid Group* Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* [10/12 à 23:02] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 *Page 08* Bayan na zauna a kusa da shi ne na ce"Qalbi ya aiki?" Murmushi ya yi ya janyo ni jikinsa ya ce"Hum yau ba kin ƙi zuwa office ba ai kin kyauta" girgiza kai na yi na ce"To Qalbi kai da ka bar ni a nan a kwance ba lafiya" da sauri ya dafe goshinsa ya ce"Ya Salam wallahi na manta da kin ce ba ki da lafiya" wani irin takaici ne ya rufe ni jin wai ya manta ma da ba ni da lafiya. Wannan wata irin rayuwa ce tashin hankali daga na uwar miji sai na mijin ni yanzu ya zan yi da raina, ganin idan na nuna ɓacin raina ma a banza sai na yi kwafa na share abin da ya faɗa tare da dane kululun baƙin cikin da ya tokare min wuya, amman duk da haka sai na yi shiru ban amsa mishi ba, sai ya kuma cewa"Ya jikin yanzu?" "Na gode wa Allah" dan shiru ne ya biyo ba sai kuma ya ce"Duk da ba ki da lafiya har da girki ki ka yi" kai na gyaɗa mishi na ce"ai bin da ya zamar min dole ne, ko ban yi don kaina ba za a saka ni na yi" "Kai Babe idan da ɗan ni ne ai da kin bari ko?" Girgiza kai na yi na ce"Ta ina zan fara bari bayan kuma na san ko breakfast ba ka yi ba da za ka fita, to wai ma me ya hana ka dawo gida da rana?" "Kin san sarai aiki ne ya yi min yawa idan ba dan haka ba ai da na dawo tunda dai na riga na san ki na gida" "To ai ka ci aikin ka koshi a office ko" gira ɗaya ya ɗaga ya ce"Sosai ma na ci na ƙoshi, yanzu kawai sai barci zan yi" ya faɗa yana wani kumshe ido kamar da gaske barcin yake ji. Tashi na yi na bar falon ɗakina na shiga na ɗauko ledar less ɗin na dawo falon na miƙa mishi na ce"Qalbi ga shi" karɓar ledar ya yi ya ce"Wannan fa daga ina?" Zama na yi na ce"Oder da na yi daga wajen Rumy ce ta ƙaraso" buɗe ledar ya yi ya fara kallon kayan ya ce"Ban fahimta ba, ba ce min ki ka guda biyar ki ka siya ba?" Gyaɗa kai na yi na ce"E biyar ne" "Amman a nan guda uku na gani ko kin kai wa Ummi ne" girgiza kai na yi na ce" Ta ina zan je gidan Ummi ban sanar da kai ba, Mama ta ɗauki guda ɗaya ta ba kawarta ɗaya" ido ya zaro kamar za su faɗo ƙasa ya ce"Ban fahimta ba a kan me Mama za ta ɗauki abin da ki ka siya da kuɗinki har kuma ma ta yi kyauta da shi" "Ba a kan komai ba, ta yi haka ne don ta isa da ni duk abin da yake nawa kamar dai mallakinta ne ai"na faɗa duk da dai raina bai so faɗin hakan ba.ta ina zan fara faɗa mishi ban ji daɗin abin da mahaifiyarsa ta yi ba, ai ko ba komai a na barin halak don kunya, tashi ya yi ya fice daga falon na kuwa san ɗakin Mama Sa'a zai je. Tsaki na yi a raina na ce"Ya rage naku less kuwa yanzu na fara siye a gidan nan" Abdallah yana fita daga ɗakin ya nufi ɗakin Mama Sa'a tare da su Jiddah ya tarar da ita Jiddah ce ta gaishe shi Rumana tana faman latsa wayarta ya ce"Ke marar kunya ban isa ki gaishe ni ba ko?" Da sauri ta ajiye wayar ta ce"Ka yi hakuri yaya Abdallah ina yini?" Banza ya yi mata bai amsa ba Mama ta ce"To mene ne kuma ƴar gwal ta ce mun yi da za ka zo ka sauke masifar a kan ƴata?" Bai bi ta kan abin da ta ce ba sai ya ce"Mama me ya sa ki ka ɗauki less ɗin Babe?" Tashi Mama ta yi zaune tana ɗaura dan kwalinta ta ce"Ban fahimta ba ita Sumayya ce ta ce maka na ɗauki kayanta" zama ya yi ya ce"Mama maganar gaskiya nake yi bai dace ki yi haka" "Oho kenan ni karya nake yi ko, matarka ita ce mai gaskiya ko ubana? Yanzu faɗa min abin da ya dace na yi, to na je na ɗauka ku yi abin da za ku yi daga kai bar ita, to in banga lalacewar zamani Abdallah yaushe ka yi girman da za ka tsaya min a ka saboda matarka" tashi ya yi ya bar ɗakin bai kuma cewa komai ya koma ɓangarensu. Yana shigo wa ya nufi wajen da sumayya ke zaune tun fitar shi ya ce"Don Allah Babe ki yi hakuri, idan na samu kuɗi zan siya miki waɗansu" girgiza kai na yi na ce"Ba na bukata Qalbi, kar ka damu kuma ina son ka bar zancen maganar ta wuce shi kenan" Washegari tunda safe Aysha ta tashi da wuri don tare da ita na yi girkin breakfast sai surutu take yi min. Bayan na gama girkin na shirya tsaf na yi mata wanka ita ma ina fita zuwa falo ta jawo kwalin madarar da ta sha tun juya sauran da na ajiye a kan mirror ta ɗauko ta yi zaman dirshan ta shiga sha. Ina dawo wa na ce"Allah mai iko na manta sam da wannan madarar da ba zan bari ki ɓata jikinki ba" daukarta na yi na goge mata jiki kafin na ɗaura ta a kan bed ɗina, daidai kuma Abdallah ya shigo ɗakin ya ce"Babe barka da safiya yau dai Aysha ta kwace min ke" dariya Aysha ta yi kamar wadda ta fahimci abin da yake nufi. Kan bed ɗin wajen da take zaune ya je ya rungume ta ya ce"Princesse bonjour/good morning" cikin hausarta da ba ta gama zama cikakkiya ba ta amsa. Nan suka hau hira ni kuwa ina gyara wajen da ta gama shan madara duk ta zubar da ita a ɗakin, don a garinta haka ta riƙa kwasa tana zuba wa a baki. Ya ce"amman yau Aysha ba ta sha madara ba ko?" Wata uwar harara na watsa mishi na ce"Ba ta sha ba kam tunda dai idonka sun makance" sai ya fashe da dariya ita ma dariya ta yi ganin Abdallah na dariya. Tsaye na yi a wajen ina kallon su ina fatan Allah ya kawo ranar da ni ma zan samu yara wanda zan yi alfahari da su kamar ko wace uwa, ni ma na ga ranar da zan wuce gorin da Mama Sa'a take yi min a gidan nan. Ban san hawaye na zuba daga idanuna ba sai jin hannun Abdallah yana share min su sai da ya gama share min hawaye ya ce"Babe me ya faru kuma kike kuka?" Girgiza kai na yi na ce"Babu komai fa" "ke Babe babu komai kike hawaye kuma?" Gyaɗa kai na yi kafin na bar wajen domin aikin banza ne idan na sanar da shi damuwa ta ba shi da maganinta Allah da ya halicce mu shi kaɗai ne zai iya kawo min mafita a halin da nake ciki a yanzu. Bayan mun gama shirin mu tun tuni Abdallah ya wuce zuwa office, ni ma hannun Aysha na kama muka sauka ƙasa inda muka tarar da Mama da ƴaƴanta suna breakfast har mun kai bakin kofa Mama ta ce"Ke sumayya tare da Aysha za ki tafi yawon gantalin?" "E Mama zan kai ta gida ne" "E to gara dai ki mayar musu da ƴarsu kar maitarki ta motsa cikin dare ki tsotse mata jini kamar yadda ki ke tsotse na ƴaƴan Abdallah, don ke kam baƙin ciki ya yi wa rayuwarki kamun kazar kuku babu abin da za ki bari wani ya samu ko wannan ɗan aikin da Abdallah yake yi don na tsaya ne ina addu'a da tun tuni kin saka an kore shi mai farar ƙafa kawai" sai da ta gama maganganunta na ja hannun Aysha muka nufi mota. Sai da ta zauna ta ce"Momy za ki kai ni gida?" "E princesse zan kai ki gida, ko bakya son zuwa" "A a Momy ni ba zan je ba" "me ya sa, daddynki zai yi missing ɗinki fa" "To ai Momyna ba ta yi missing ɗina ba" girgiza kai na yi na ce"Ki bar faɗin haka Princesse Momynki time ne ba ta da amman idan ba haka ba ta yi missing ɗinki sosai" gyaɗa kai ta yi kafin ta ci gaba da wasa da wayata da ke hannunta. Sai da na biya office na ba secrétaire ɗin aikin da na yi jinya kafin na fito na nufi gidanmu. Da sallama na shiga dakin bayan mai gadi ya buɗe min gate ɗin gidan ina riƙe da hannun Aysha. Ummi da ke zaune a dakin ta ɗago ta amsa. Littafin da ke hannunta ta ajiye tare da rungume Aysha ta ce"Ga kishiya ta zo har gida" zama na yi na ce"Ummi ina kwana?" "A gidanki Aysha ta kwana?" Gyaɗa kai na yi ina jin zafi a raina don babu shakka ba dan Ummi ba ta ji gaisuwa ta ba ne sai dai kawai ba ta yi niyyar amsa min ba ne. Tsawon shekaru huɗu kenan da Ummu ke fushi da ni har yanzu ina jin ɗacin abin a cikin raina sai dai kuma duk da haka ban bar bata kulawa kamar yadda na dauki lokaci mai tsawo ina yi. Sai yanzu na dawo daga duniyar tunanina na ce"E Ummi jiya Mustapha ya je da ita sai ya bar ta" "Ina ita Rumy take?" "Ba mu haɗu ba, ni ma yanzu daga office nake zan kai Aysha gida ne" "Ai yanzu kin san sarai Rumy ba ta gida" wasa na fara da yan yatsuna na ce"E dama sai da yamma zan kai ta za mu zauna a nan ne" "Ki bari zan kira Rumy ta zo ta ɗauke ta za ki iya tashi ki koma bakin aikinki" murya na ɗan rawa na ce"Ummi ina mai ƙara ba ki hakuri a kan Kuskurena amman zuciyata ba za ta iya ci gaba da ɗaukar irin wannan hukunci da kike yi min Ummi ke uwata ta ce kaf duniya ba ni da wanda ya fi ki. Na san na yi kuskure dan Allah Ummi ki yafe min" ɗaga min hannu ta yi ta ce"Sumy ya isa haka idan ba ki da abin cewa ina son ki kama gabanki, tabbas dan na san muhimmancin bakin uwa da tasirin da yake yi a kan rayuwar ƴaƴanta idan ba haka ba da na daɗe da cire ki daga cikin ƴaƴana, ba zan yi miki mugun fata ba kamar yadda nake sanar da ke a kullum sai dai na yi miki fatan shiriya" idanuna tun tuni sun cika da hawaye ajiye ledar less ɗin da zan kawo mata na yi kafin na ajiye mata kudi

Chapter 4 of 8