Share this page
5 / 8
da za su kai jika ɗari biyu na ce"Ummi Allah ya huci zuciyarki, ko ki na bukatar wani abu?" Girgiza kai ta yi ta ce"Babu abin da nake bukata za ki iya tafiya" miƙe wa na yi sai na sumbaci Aysha a goshi kafin na fice daga falon. Ina shiga motata sai na haɗe kaina da sitiyarin motar na fashe da kuka mai tsuma zuciya, tsawon shekaru huɗu kenan ina abu daya, tsawon wannan lokaci a duk sanda zan zo ganin Ummina zan nemi yafiyarta a kan laifina sai dai kuma har yanzu jiya-i-yau ba ta ma kallona bare har na saka ran za ta saurare ni har ta yafe min laifin da Allah ne kaɗai masanin abin da ke ɓoye. Sai da na yi kukana mai isa ta kafin na share hawayena na yi wa motar key sai office ɗina domin ban san inda an nufa ba kamar yadda na yi wa Mustapha alkawarin yi wa Rumy magana ban iya zuwa shagonta ba domin bana cikin nutsuwar da zan iya fahimtar da ita Kuskurenta. ★Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Cmnts nd share* [11/12 à 22:44] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 09* Ko a office ɗin ma haka na yini cikin rashin sukunin da rashin madogara. Duk abin da nake yi maganganu Ummina su na maƙale a cikin zuciya ta. Na rasa yadda zan yi don Ummina ta yafe min kuskuren da gabadaya duniya ke kallona da shi. Abdallah ne ya shigo office ɗin yau kam ya yi sallama kuma ko da ma bai yi ba yau ba zan tanka mishi ba. Zama ya yi ya ce"Kin je ganin Ummi?" "E na ja ban ma karasa ba wajen Rumy Ummi ce ta ce na bar Princesse a wajenta" shiru ya yi yana bin fuskata da kallo ya ce"Ki yi hakuri Babe duk wannan abin da yake faruwa ni ne na ja miki shi idan da a ce ban bi son da zuciyata ke yi miki ba da yanzu duk haka ba za ta riƙa faruwa ba" da sauri na saka hannu na rufe mishi baki. Cikin Muryar kuka na ce"Hakika Qalbi soyayyar da muke yi wa junan mu ba za ta zama zunubi ko kuskuren da wadannan abubuwan suke faruwa ba, duk wani abu da ka gani Allah ya riga ya saka shi a cikin kundin kaddararmu ne babu yadda za mu yi da shi sai dai mu yi addu'a kuma mu zuba wa sarautar Allah ido" shiru ne ya biyo baya na wani dan lokaci. "Babe ki ba ni dama na sawake miki, domin ina son ganinki cikin farin ciki ina son ganin kin yi rayuwa kamar kowa, ki amince min na sake ki sai ki auri wani" na ji muryar Abdallah kamar saukar guduma a tsakiyar kunnena bayan shiru ya biyo baya na wani dan lokaci. Cikin hanzari na ce"Hakika ba ni da wani miji a wannan duniyar idan ba kai ba, muddin ka ga na kasance da wani ɗa namiji to sai dai idan babu kai maganar saki ka cire ta daga tunaninka. Ranar da Allah ya ƙaddara karshen aurenmu tabbas na san zai dauki ran daya daga cikinmu ne" na faɗa ina ci gaba da zubar da hawaye tabbas na san rabuwar mu shi ne mafita a gare mu amman tabbas soyayyar da muke yi wa juna idan har muka yi kuskuren rabuwa to babu shakka karshen farin cikin da za mu yi kenan a wannan duniya. Mu ɗin mun zama hanta da jini rabuwar mu zai yi wuya, domin kuwa mun rasa wani bangare ne na jikinmu. Shiru ne ya biyo baya na tsawon wani lokaci duk da dai ban san me Abdallah yake tunani ba na san ba zai wuce mafita yake hango mana a rayuwar aurenmu duk da dai na dogara akan babu mai yi sai Allah, ido kawai na zuba mishi ina jiran jin ranar da zai yi niyyar katse tunanin da yake don yi min magana. "Babe ko za mu sake komawa asibiti ne? Kin san fa an ce shi magani katari ne sai ki ga kuma an dace da samun waraka" ya faɗa yana kokarin janye idanunsa daga kaina don da dukan alamu kunya ce ta kama shi. "koma wa asibiti ba mafita ba ne a gare mu, wata asibitin ce ba mu je ba? Qalbi sanin kan ka ne kuɗin da muka kashe akan matsalarmu Allah ne kaɗai ya san adadin su, sun ishi wani mai karamin karfin ci da sha har da sana'a" shiru na yi na dan lokaci amman ganin ba shi da niyyar amsa min sai na ci gaba da maganata "Kamar yadda na faɗa maka, Allah shi ne mai saukar da cuta, mai kuma bada lafiya a lokacin da ya so, mu tattara duk lamuranmu mu saka su a hannunsa tabbas shi ɗin mai ji ne kuma mai gani ne ya fi mu sanin halin da muke ciki sannan ya fi mu sanin tanadin da ya yi wa rayuwarmu a nan gaba, kila ma duk wannan burin samun lafiyar da gare mu akan matsalar da ta adabe mu sau ka ga mafitar ba alkairi ba ce" A hankali ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya nufi inda nake zaune ya rungume ni yana mai share min hawaye ya ce"Hakika Babe na yi dacen samun ki, kuma na san Allah ne ya yi min alfarma ya bani ke ba wai tsumina ko dabarata ba ne, ina fatan mutuwa in bar ki Babe don tabbas idan ki ka mutu ki bar ni na zama maraya na har Abada" rungume shi na yi ni ma a jikina ina mai ci gaba da zubar da hawaye wanda suka zamar min kamar wata kankara da ke sanyaya zuciyata. Zame jikinsa ya yi daga nawa ya saka hannunsa yana goge ruwan hawayen da ya ɓata min fuska. Kofar aka kwankwasa na bada izinin shigowa. Mustapha ne ya shigo da sallama ya ce"To tantabaru ku yi mana uzuri dan Allah don a office kuke ba a bedroom ɗinku ba" murmushi na yi don idan da sabo mun saba da halinsa Abdallah ya ce"Kai malam ba ka je office ba?" Girgiza kai ya yi ya ce"Daga can nake, Sumy wajen ki aka aiko ni" dariyata na kunshe don ganin irin rainin hankalin Rumy ta ina za ta fara aikin shi bayan kuma ta san lokacin yana office. "To me aka ce na yi?" Na faɗa ina bin shi da kallo "Ta kira wayarki ne tun ɗazu ba ta same ki ba, ta ce kar ki kawo princesse yau ki bar ta sai weekend" "To ai an yi aikin banza don har na kai ta gida wajen Ummi kuma ta ce za ta kira ta don ta zo ta ɗauke ta" girgiza kai ya yi ya ce"Ni kam yanzu ban san yadda zan yi ba" Abdallah ne ya ce"Ka koma bakin aikinka zan je na ɗauko ta zuwa an jima" murmushi ya yi ya ce"yauwa haka ya yi na gode sosai brother" a tare suka bar office ni kuma na fara tunanin akan wane dalili za ta ce kar a kai yarinyar gida bayan kuma ita tana nan ba komai take yi ba. Wayata da tun bayan barin gidan Ummi take cikin mota na sauka ƙasa parking Space na dauko ta. Kiran Rumy na gani babu adadi kiranta na yi ringin biyu ta ɗaga na ce"Rumaisa akan wane dalili ki ka ce kar a kai Princesse gida" cikin halin ko in kula ta ce"Tafiya zan yi zuwa wani taron kasuwanci" rai a bace na ce"Rumy zaman aure da kike gani ba abin wasa ba ne, ko sati biyu ba a yi ba da kika dawo daga yawon ki yanzu kuma za ki koma. Haba dan Allah ko ba ki ji tausayin Mustapha a matsayinsa na mijinki ba ya dace a ce kin ji tausayin Aysha a matsayinta na ƴarki mai ƙananun shekaru wannan sam ba halin uwa ta gari ba ce" "ke dan Allah Sumy tsaya ke kin san mene ne uwa ma bare kuma har ki ce wa wani shi ba uwa ta gari ba ce, ke da kike ta garin ina ƴaƴanki suke? Ina son ki sani ba ki fini son Aysha ba don ko babu komai daga tsatsona ta fito ni na yi rainon cikinta. Idan kin ga kin iya riƙe ta har na dawo to idan ba za ki iya ba kuma zan bar ta a wajen mahaifinta. To in ban da abin ki ai ni taimakon ki ne zan yi yadda ba ki da wanda za su ɓata miki ɗaki shi ne na baki aro amman ki zo ki dame ni da wata nasiha ban ci ban sha ba. Ki ji da matsalar gabanki mana ki ji da matsalar rashin haihuwar da ta yi miki kamun kazar kuku" daga nan ta kashe wayar kit. Da mamaki nake bin wayar da kallo, tamkar wani audio haka maganganunta suke dawo wa a cikin kunnena. Na rasa ma abin da yake min daɗi ko office ɗin ƙasa komawa na yi na figi motata na nufi gida. Ina isa gidan kai tsaye dakina na nufa ban tsaye bin ta kan Mama Sa'a da ke falon ba tana yi min magana. Kwanciya na yi akan gadon ina tunanin rayuwar da muka yi a baya. Rumaissa na kashe kiran da ta yi wa Sumayya dai ta kira wata number wadda da dukan alamu ba ma ta Niger ba ce. Rai a matukar ɓace ta fara magana mai kama da faɗa "Kin ga abin da ƴar gwal ɗinkin ta yi min ko?" Daga can bangare aka amsa mata da "Me kuma ya faru? Mene ne abin da Sumayya ta yi miki yanzu?" Kamar wadda za ta mangare mutum ta ce"Ta fara yi min katsaladan ne a cikin rayuwar aurena, wallahi ki faɗa mata hawainiyarta ta kiyayi rama ta to kin san sarai ba ni da mutunci" cikin kwantar da murya matar ta ce"Rumaissa ki yi hakuri idan dai Sumayya ce zan yi mata magana kuma in sha Allah ba za ta sake saka baki a cikin lamarin aurenki ba, haka ya yi miki?" Gyaɗa kai Rumy ta yi ta ce"E hakan ya yi mu kwana lafiya" tana gama maganar ta katse kiran. Tunani matar ta shiga yi akan wane irin laifi ne kuma Sumayya ta yi da har Rumaissa ta kawo kashe, don ita rabon da ta ga kiran Rumaisa har ta manta. Tsaki ta ja tana cewa "kila ma ba wani abun a zo a gani ta yi mata ba amman kuma ta ɗaga wa mutane hankali a banza" Na yi nisa cikin tunanina na ji wayata tana ringin ɗaga kaina na yi sai na ga number anty Maryam yayarmu ce ita ce ta farko a cikin ƴaƴan Ummi tana ƙasar Canada da mijinta da yaranta guda biyu. Da sauri na ɗaga kiran tare da yin sallama na ce"Anty ina yini?" "Lafiya qlau, Sumayya ya aiki?" "Aiki kam da godiya, ya yara?" "Duk suna lafiya, me ya faru tsakaninki da ƴar uwarki?" Da sauri na tashi zaune daga kwanciyar da nake don na yi mamakin tambayar da ta yi min. "Anty me ya faru? Wani abu aka ce na yi?" Na faɗa da sauri don har na matsu don jin amsar da za ta bayar don ban san abin da Rumaisa ta ce na yi ba. "Rumaissa ta ce min ki na yi mata shiga hanci da ƙudundune a rayuwar aurenta bayan kuma ban san ki da saka kanki a cikin abin da bai shafe ki ba shi ya sa nake son jin gaskiyar lamarin?" Na shiga uku ni Sumayya wannan wata irin rayuwa ce laifin me na yi wa Rumy har take tunanin na shiga rayuwar aurenta ni kuma. "Anty wallahi ba haka ba ne kawai don na faɗa mata gaskiya ne akan yawan yawon da take yi ba ta tsayawa ta kula da ƴarta da mijinta shi kenan na yi mata laifi" na faɗa wannan karon har da hawayena ina jin wani iri a cikin raina, yau ko wani na ga yana shirin shiga rayuwar aurenta ai zan hana shi bare kuma a ce ni da kaina zan shiga har na yi mata katsaladan abin da cin rai yake. "Sumayya kin san sarai tun ba yau ba na shiga tsakaninku da Rumaisa, ki fita harkar ta mana idan ta bukaci wani abu daga gare ki sai ki yi mata idan ba haka ba kuwa ki kawo ido ki zuba mata kin fi kowa sanin yadda take wata irin mutum ce ita da ba za ka taɓa fahimtar abin da take so idan ba ta faɗa maka, tunda dai har gyara kayanka ya zama sauke mu raba zuba mata ido akwai ranar da za ta fahimci don ki na masoyiyarta ne kike faɗa mata wasu abubuwan ba masu kyau ba ne ta daina aika su. Shi kuwa namiji duk yadda ya kai ga son ka idan ba ya samun kwanciyar hankali dole ne wata rana ta zo da zai daina son ka" hawayen baƙin cikin da suka zubo min na share na ce"Shi kenan anty babu komai zan bar faɗa mata gaskiya tunda ba ta so" "Yauwa Sumayya hakan zai fi kawai, ya maganar neman maganin ke da Abdallah" cike da kunya da kuma jin nauyi saboda idan har ba da Abdallah ba ne, ba na son yin maganar rashin haihuwa da kowa. Ɗaurewa na yi na ce"Mu na kan neman magani har yanzu" ajiyar zuciya ta sauke ta ce"Allah ya kai mu ranar da zai ba ku na ku ƴaran kuma ku huta" da amine na amsa sai kuma shiru ya biyo ba can ta ce"To ki gaida Abdallah sai kwana biyu in sha Allah" kashe wayar ta yi sai na bi wayar da ido ina mai nazarin lamarin yar uwata Rumaissa. *Cmnts nd share* [12/12 à 18:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 🔥FREE PAGE🔥 NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA? Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange. *Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252* *Page 10* Ganin dai babu sarki sai Allah, sai na tashi na shiga toilet na yi wanka na fito na tada sallah. Bayan na gama sallar sai ga Abdallah ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da Aysha, da sauri ta sauko daga hannunsa ta yo wajena. Ni ma miƙewa tsaye na yi ina naɗe abin sallah ina faɗar "Oyoyo oyoyo princesse ta dawo" zuwa ta yi inda nake tsaye tana nuna min hannunta mai ɗauke da chocolat na ce"Wa ya ba ki abin daɗi haka?" Da hannu ta yi min nuni da Abdallah da ke tsaye a bakin kofa har yanzu bai motsa ba bare kuma ya yi magana na ce"Ni ma uncle a ba ni chocolat" da sauri ta ɓoye nata a bayanta ta ce"Momy babu" dariya na yi na jawo ta jikina na rungume ta. Duk wani kunci da damuwar da nake ciki sai na ji kamar an yaye min shi babu ko ɗaya sai wani daɗi da nake ji domin murmsuhin Aysha yana saka ni farin ciki fiye da misali. Har yanzu murmsuhin kan fuskata bai gushe ba sai na kalli Abdallah na ce"Qalbi sannu da zuwa ina chocolat ɗina?" Karasowa ya yi cikin dakin ya ce"Ba a ba manya iya na yara ne" girgiza kai na yi na ce"To ai ni ma yarinya ce, ko Aysha?" Da sauri ta girgiza kai ta ce"A a Momy ba yarinya ba ce" dariya Abdallah ya yi ya ce"To kin ga ni ko Aysha ai ta san ke ba yarinya ba ce, kin ga kuwa ai ba za ki samu chocolat ba" Dariya na yi na ja hannunta ina cewa"Mu je a yi wanka tunda dai an gama kwadayin" da gudu ta ruga ta ɓoye a bayan Abdallah tana noke kafaɗa "Ikon Allah wannan duk gudun wankan ne?" Da sauri ta gyad'a kai tana ta dariya. Sai da na haɗa da wayo kafin ta yarda ta bi ni zuwa toilet don yi mata wanka. Ko da na gama na canza mata kaya na shafa mata mai da turare sai na bata wayata na nufi dakin Abdallah, akan gadonsa na tarar da shi yana zaune ya rafka uban tagumi toilet dinsa na wuce kai tsaye na haɗa mishi ruwan wanka na zo na zauna a kusa da shi na ce"Me yake damunka Qalbi, wannan uban tagumi da ka rafka?" Girgiza kai ya yi ya ce"Babu komai Babe" kasa na yi da murya na ce"Ai banza ba ta kai zomo kasuwa, sai dai kuma idan ita damuwar ta kai girman da ba za a iya sanar da ni wanzuwarta ba" shiru ya yi bai ce min komai. Na kuma cewa"Tashi ka je ka yi wanka Allah ya yi maka maganin damuwarka" Tashi ya yi ya nufi bathroom ni kuwa na koma ɗakina na shiga ba Aysha abinci don na san daga wannan game ɗin za ta bige da yin barci. Ina gama bata abinci a baki tana ci tana zuba min shagwaɓa har ta gama na yi mata brush ta dawo kan bed ɗin ta zauna. Cire mata game ɗin na yi daga wayar na saka mata application ɗin da aka tanada domin yara don su koyi addu'oi. Rufe kofar na yi kafin na koma dakin Abdallah. "Qalbi mu je ƙasa ka ci abinci mana" lura na yi da bai ma san ina yi ba har sai da na karasa gaban shi na saka hannuna ɗaya a tsakiyar sumar kansa na fara shafa wa a hankali. Sai yanzu ya ɗago kai ya kalle ni ya ce"Babe yaushe ki ka shigo?" "Tun ɗazu na shigo ina yi ma magana sai na lura ka yi nisan kiwo" shiru ya yi bai ce min komai ba sai na kuma daurewa na ce"Dama ina yi maka magana ne akan ka zo mu ci abinci" Buɗe bakinsa ya yi da niyyar ya yi magana sai kuma ya fasa, lura da kamar akwai abin da yake son sanar min da na yi sai na zauna a bakin gadon na haɗa hannunsa guda biyu a cikin nawa a hankali na fara matsa masa su. Na dan ɗauki lokaci ina yin haka kafin na ce"Qalbi ni fa rufin asirinka ce idan ba ka faɗa min abin da yake damunka ba wa za ka faɗa wa?" Ɗago idonsa ya yi ya sauke su a kaina sai da ya ƙare min kallon don har na yanke shawarar watsar da makaman yaƙina na ƙyale shi saboda ba karamin yaro ba ne shi ɗin da zan zauna ina ta faman rarrashin shi akan abin da yake damuwarsa ce, a iya sani na da shi ban aikata mishi laifin komai bare kuma na zargi kaina da cewa na yi mishi laifi. Sai dai kuma kwatsam a lokacin da ban yi zato ba na ji ya ce"Babe ina da wata ƴar bukata ce a wajenki" ido na zuba mishi ina bin shi da kallo kuma na buɗe kunnena da kyau. "Yaya Hisham ne aka kora daga gidan da yake haya shi da matarsa, to kuma nan za su dawo da zama" Da ido kawai nake bin shi da kallo don ban ma amsa ba, ban ma san mene ne amsar da ya dace na bashi ba don wannan maganar tashi ta fi kama da sanarwa akan neman izini ko babu komai shawara tana da daɗi sai a yi min shawara amman haka kawai a ce min za su dawo gidan ai ba ni da ta cewa tunda dai har sun riga da sun yanke hukuncinsu. Sai kuma na ji yana cewa"Bai biya kuɗin hayar wata uku ba mai gidan ya ce zai kai shi kotu idan bai biya shi ba zuwa karshen wannan satin, ina son ki bani aron jika ɗari biyar don Allah Babe, ba zan so a kai shi kotu ba saboda matsalar kuɗi" gyaɗa kaina na yi na ce"Allah ya kai mu gobe zan maka transfert" da sauri ya rungume ni ya ce"Babe na gode sosai Allah ya bar kauna" ban amsa mishi don gaskiya ban ji daɗin abin da ya yi min ba. "Tashi mu je ka ci abinci" miƙe wa ya yi ya kama hannuna muka sauka ƙasa don cin abinci. A dinning gabadaya jama'ar gidan suka haɗu don cin abincin dare. Bayan na zuba ma Abdallah na zuba na Mama da na Baba sai na zuba wanda zan ci na zauna akan kujera na fara ci. Sai na ji Mama tana cewa Baba"Mun gama magana da Hisham ɗin gobe idan Allah ya kai mu za su taho nan ɗin" ni dai ban tanka musu ba na yi shiru na ƙyale su ina ci gaba da cin abincina. Sai Mama ta ce"Sumayya gobe idan Allah ya kaimu su Hisham za su dawo nan da zama gobe idan Allah ya kai mu sai ki share musu wancan ɗakin" da sauri na dago kaina ina bin yatsarta da kallo sai na ce"Ai gobe zan je office ne" Wani banzan kallo Mama ta watso min ta ce"Aikin banza wane ne ya damu da zuwa office ɗinki babu wani office da za ki je muddin dai ba ki gama aikin da na saka ki ba" tashi na yi na bar dinning ɗin ganin wanda nake zaune don shi bai damu ya saka baki ba a cikin lamarin ba. Ina shiga ɗakina na yi wanka na yi addu'a tare da yi wa Aysha na kashe wayata da take ta faman karatun addu'a don tun tuni Aysha ta yi barci. Kafin Ni ma na kwanta na rufe idona ta tunanin mafita don na fara gajiya da wannan cin kashin da ake yi min a gidan mijina. Washegari ko da na farka breakfast na daura har yanzu Aysha ba ta farka ba shi kuwa Abdallah ko ta kanshi ban bi sai da na gama duk aikin da zan yi na haɗa breakfast ɗinsa na kai mishi ɗaki sai a lokacin na ce"Qalbi barka da safiya" "Jiya ko da na shigo kin yi barci ko?" Gyada kai na yi na ce" gajiya ce ta saka ni gaba, ga abinci ka ci don kar ka yi lati" Zama ya yi ya fara cin abincin ya ce"Yana na ga kin shirya yau ba za ki je office ba ai ko?" Da mamaki na kalle shi na ce"Akan me ba zan je office ɗin ba?" Cikin halin ko in kula ya ce"Ai umarnin Mama ne ba ta ce kar ki je ba ki zauna don gyara wa su yaya ɗaki ba?" Wani shu'umin murmushi na yi na ce"E kuma haka ne, bari na je na duba Aysha ko ta farka daga barci" ɗakina na shiga ina saka yadda zan yi kafin na dauki Aysha na kaita toilet na zuba mata ruwa a hankali a fuska. Tashi ta yi ta buɗe ido tare da fashe wa da kuka na ce"Zan yi miki video na ce da uncle kukan wanka kike yi" sai ta yi shiru da bakinta na

Chapter 5 of 8