ga kuma ina jin nauyin mahaifinta. Ban san Qalbi ya karaso cikin falon ba sai da ya taɓa min kafaɗa na dago na kalle shi ya ce"Ki yi hakuri Babe amman ba na nufin na amince akan ki kai Aysha gida domin na san yadda kike jin farin ciki idan ki na tare da ita ba zan so na zama sanadiyar da zai datse ba" murmushi da ya fi kuka ciwo na yi na ce"ka kwantar da hankalinka zan kai ta gida kamar yadda Mama ta bukata idan ina bukatar ganinta don na yi farin ciki zan je gidansu" daga haka na tashi na bar mishi falon zuwa ɗakina.
*SAURA PAGE UKU MU GAMA FREE PAGE*
*Cmnts nd share*
[18/12 à 21:46] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780416252
🔥FREE PAGE🔥
NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?
Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.
*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*
Saura page biyu na gama free page ki hanzarta biyan kudin karatun ku
*Page 13*
Zama ya yi a wajen tare da zabga uban tagumi shi kansa ya san abu ne mai wuya Mama ta saka Sumayya musamman a yadda Sumayya ke son Aysha sannan take jin nauyin Mustapha ba za ta iya kiransa akan ya ɗauke ƴarsa ba. Ya daɗe a wajen a zaune yana saƙa da warwara har wani barci ya fara kokarin dauke shi sai ya tashi ya nufi ɗakinsa. Yau kam ko ta kan abincin da Sumayyar ta girka basu bi ba su Mama ne kaɗai suka zauna suka ci iya cikinsu kafin suka bar shi a nan.
Washegari tun bayan da Abdallah ya tashi ya ma ƙasa haɗa ido da Sumayya don wasan ɓuya ya shiga yi mata wani bala'in kunyarta yake ji bai ma san ta ina zai fara tunkarar ta amman kuma ya san babu shakka sai Sumayya ta cika umarnin da Mama ta bayar don ko shi bai isa ya tsallake umarninta ba.
★Sumayya★
Ina tashi daga barci bayan na yi sallah da addu'oina na shiga wanka sai da na yi wanka kafin na sauka ƙasa don yin breakfast Mama na tarar a falo tana faman kallon tv cikin raina na ce"Ikon Allah ko dai a falo ta kwana yau?" Ganin babu mai bani amsa sai kawai na ce"Mama ina kwana ?" Ɗago kai ta yi ta lalle ni ta ce"To mai sunan mayu an tashi kenan" gyaɗa kai na yi alamar haka ne sai ta ce"Allah na tuba yo ke sumayya ai mantawa nake yi duk wannan abin da Abdallah yake na riga na san ba yin kansa ba ne shi da ya auri mayu ai sai abin da aka gani, kuma fa ni haihuwar ma na fara zargin idan ba ke ce kike sadaukar da yaran tun suna gudan jini kafin su zama tsoka ga aljanunku na mayu don maye kam abin tsoro ne" tashin hankali daga tashi na daga barci ko wanda na zo gidan don shi ban gani ba amman na fara breakfast da mugayen maganganu sai kuma ta ci gaba da cewa"Wannan karon dai don Allah idan kin samu ciki ki yi hakuri kar ki kai musu ki bar mana shi muna bukatarsa" tashi tsaye na ina jin hawayen bakin ciki su na son zubo min sai dai kuma alkawari na ɗauka akan ba zan taɓa barin Mama Sa'a ta ga hawayena ba har ta yi tunanin ta yi galaba ne a kaina sai dai kuma ba a san maci tuwo ba ba zan taɓa karaya har ranar da Mama Sa'a za ta daina yi min cin fuskar da take yi min a gidan nan.
"Na shiga uku don na fahimci ke maya ce da sunan mayu shi ne ki ka tsura min ido ni ma za ki zuƙe min jinina ta hanyar maitar ido ko? To sumayya a hir din ki kurwata ba abin wasan mayu ba ce, to idan ba lalacewa irin ta duniya ba don tsabagen jaraba jinin surukarki za ki sha yanzu kuma" murya Mama Sa'a ce ta katse min tunanin da na yi nisa a cikinsa sai da ta kai aya a maganarta kafin na mike na nufi kitchen don ɗaura abincin safe yau idan da ba uwar mijina ba ce ta yi min kazafin maita da babu shakka kotu ce za ta raba mu da shi amman ita Mama ta zama kuturwar uwa zama da ita dole ne. Bayan na bar falon hawayen baƙin ciki suka kuma zubo min amman sai na share na shiga girkina.
Ina cikin aikin gabana sai ga Umaimah ta shigo kitchen ɗin ta ce"Barka da Safiya Hajiya Sumayya" dan murmushin takaici na yi na ce"Barka da asuba Umaimah" sai ta fara yan dube-dube a kitchen ɗin na ce"Umaimah me kike nema ne haka?" Shiru ta yi min ba ta amsa min ba ni kuwa sai na ja bakina na yi shiru domin kar na jaza wa kaina da wannan safiyar.
Sai da ta gama dube-duben amman ba ta samu abin da ta zo nema ba kamar an yi mata dole sai ta ce"Juya ba ki ga sugar ba?"
Ni ɗin ma banza na yi mata kamar yadda ta yi min ɗazu ta kuma cewa "Juya magana nake yi miki fa" sai yanzu na juyo na kalle ta na ce"Umaimah a iya sani na ba sunana ba juya, sannan kuma idan kin kira ni da juya ke kuma a kira ki da me? Me lalataciyar mahaifa ko da wane suna ki ka ga ya dace a kira ki? Ba zan zauna ki saka ni gaba ki na zagina ba bayan kuma Ni ban ga yaron da aka nuna aka ce wannan Umaimah ce ta haife shi ba ni kuwa tunda dai har ban ga na ki ba gabadayanmu juya muke babu wani bambanci". Fice wa Umaimah ta yi daga kitchen ɗin tare da fashe wa da kuka. Mama ta fito da sauri har tana tuntuɓe ta ce"Subhanallah Umaimah me yake faruwa?" Cikin kuka Umaimah ta ce"Mama wallahi Sumayya ce ta shiga zagina da farar safiyar nan" cike da masifa Mama ta gyara ɗaurin dankwalinta ta ce"Me ta ce miki wannan matsiyaciyar kuma" tana mai ci gaba da kukanta ta ce"Mama yau Sumayya ta yi min gori akan haihuwa" carab Mama ta ce" ku ji gorin daura karfin zuciya to ita ɗin idan ba juya ba ce da wane suna za a kira ta, Allah na tuba tun da ta zo gidan nan ta taɓa yin ɓarin ciki ne ko kuma ta haifa ya mace ne? Babu ko ɗaya kenan kuwa ba ta isa ta ce miki juya ba don ita ta fi uwar juya ma ke ni fa ina ga tsabar son kuɗi irin nata siyar da mahaifarta ta yi ga shi yanzu Abdallah ya auro mana jaraba da kuɗinsa"
Tun farkon maganganunta har ta kai karshe ina daga jikin kofa ina jinta ina zubar da hawaye baƙin ciƙin zagin da Mama take jero min hannu na saka na goge hawayena sai kuwa muka haɗa ido da Mama ta ce"To baƙar munafuka mai baƙar aniya kin gama zagin ta kuma kin zo ki na yi mana laɓe, to fito ki faɗa min akan wane dalili za ki zage ta ke uban wa ya zage ki? Na riga na san Sumayya ba ki gadon mutuncin ba kuma wallahi ina daidai da duk wani iskanci da ki ka tsiro da shi a gidan nan, kenan tunda dai ba ki sami damar zagina shi ne ki ka ɓiye a bayan Umaimah kike zagar min ita ko?" Da sauri na girgiza kaina sai kuma ta ja tsaki ta kama hannun Umaimah kamar wata karamar yarinya suka bar falon, kitchen na koma na ci gaba da aikin gabana.
Bayan mun gama breakfast na shirya Aysha muka sauko ƙasa don zuwa office sai muka haɗu da Mama a falo ta ce"Mai babban suna yau za ki tafi gida ko?" Da sauri Aysha ta girgiza ta ce"A a ni a wajen Momy zan zauna" murmushi Mama ta yi ta ce"Hum yau kam sai kwana a gidan Momy Rumaisa" fashe wa Aysha ta yi da kuka ita kuwa Mama ta fara dariya na ja hannunta muka fito waje na ce"Princesse ki daina kuka wasa ne Mama take yi miki fa" maƙale kafaɗa ta yi ta ce"Ni dai a a" na ce"Da gaske fa ba ki ga ko kayanki ba mu ɗauko ba?" Sai ta gyaɗa min kai na ce"To share hawayenki babu inda za ki je ki na tare da Momynki kin ji?" Da sauri ta gyaɗa min kai tana murmushi kuma tana saka hannu tana goge hawayen da ya zubo mata. Shiru na yi ina bin ta da kallon tausayi gani a tsaka mai wuya ko ita Ayshar ba ta son zuwa gidansu bare kuma ni da ta zamar min sanyi idaniya sai da ta ce"Momy na bar kuka mu tafi office yau zan taya ki aiki" motar muka shiga har na fara driving sai ta ce"Momy Ni ma zan je makaranta" na ce"To ki bari sai kin kai shekara biyar" da yatsunta ta yi min nuni ta ce "shekara haka?" Na girgiza kai na yi mata nuni da alamar biyar da hannuna na ce"A a shekara haka" sai kuma ta yi shiru har muka karaso bakin office ɗin, ina kokarin shiga cikin Company wayata ta ɗauki ringin ɗaga wa na yi tare da sallama Mustapha ne na shiga gaishe shi na ce"Ina Hajiya Rumy ya dawo ne?" "A a ba ta dawo ba dama ta ce ne mu zo mu same ta a can" cike da mamaki na ce"Ban gane ba idan ka tafi aikinka fa?" "Wallahi na faɗa mata amman ta ce babu ruwanta tana bukatar ganin mu" "idan tana bukatar ganinku ta dawo gida mana" shiru ya yi na ce"Mustapha wallahi rayuwar aure ba za ta yi a haka ba kai ne namiji a gidan kai ya dace ka riƙa bada umarni ba wai a riƙa baka ba" "Sumayya ya zan yi?" Tsaki na yi yadda ba zai ji Ni ba na ce"To wai kai Mustapha ina dalilin wannan rayuwar da ka ɗaura kan ka a cikin ta? Rumy ma haihuwarta aka yi ba ita ta haifi kanta ba ka je ka sanar da Ummi abin da yake faruwa mana" shiru ya ɗan yi alamar yana nazari ya ce"Ina tsoron sanar da Ummi ne kuma a yi mata faɗa ba za ta ji daɗi ba" taɓe baki na yi na ce"Zauna a haka to, yaushe za ku tafi" "Yau jirginmu zai tashi zan zo na dauki Aysha" gyaɗa kai na yi na ce"Muna office sai ka zo, zan je gidan na haɗa mata kaya zuwa an jima ka ba mai gadi key din gidan da na ɗakinta kuma" da to ya amsa kafin muka yi sallama na kalle ta na ce"Kin yi missing ɗin daddy ko?" Ɗaga min kai ta yi alamar haka ne sai na ce"Daddy zai zo ya ɗauke ki ku shiga jirgi" ido ta zaro ta ce"Momy zan je" na yi murmushi na ce"To shi kenan sai daddy ya zo bari mu je mu yi aiki a office kafin daddy ya iso" wata irin ajiyar zuciya na sauke don ganin na samu hanyar da zan kai aysha wajen mahaifinta ba tare da raina ya ɓaci ba ko kuma na ji kunyar Mustapha.
Ina ɗan rage aikin gabana na sauki Aysha muka nufi gidan Mustapha key na amsa a wajen mai gadin kafin na shiga gidan dakinta na shiga na fara haɗa mata kayanta da na ɗauko sai ta ce ba ta son wannan daƙyar na samu na gama duk na bi na gaji. Sai ga kiran Mustapha ya shigo wayata tambaya ta ya yi ina office na ce"A a gamu a gidanka na gama haɗa kayan princesse" "To shi kenan gani nan zuwa don yanzu zamu wuce" jan hannunta na yi muka fito bakin get na ce"Princesse yanzu daddy zai zo ku tafi" gyada kai ta yi daidai Mustapha ya yi parking motarsa a kofar gidan yana fitowa da gudu ta je ta rungume shi ta ce"Daddyna" shi ma rungume ta ya yi yana murmushi cike da tausayi nake kallon su.
Karasowa ya yi wajen da nake tsaye muka kuma gaisawa kafin na ce"To Allah ya tsare hanya Ni zan koma office" murmushi ya yi ya ce"Na gode sosai Sumayya da wannan karamci da kike yi min a wannan rayuwar" "babu komai Mustapha yi wa kai ne kuma ma ai Aysha ni ma ƴata ce" kai ya gyada ya ce"Duk da haka Sumayya kin kai abin a jinjina miki" na ce"Princesse kin kawo min tsaraba ko?" Ciki da murna ta ce"E Momy zan kawo miki mana" rungume ta na yi na yi mata kiss a goshi na ce"Allah ya tsare hanya ki gaishe da Mama Rumy" sallama na yi musu kafin na shiga motata na bar kofar gidan.
*Cmnts nd share*
[19/12 à 22:38] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780416252
🔥FREE PAGE🔥
NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?
Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.
*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*
Gobe zan gama free page in sha Allah. Ku biya kuɗinku don a yi wannan tafiyar da ku.
*Page 14*
Sumayya na barin wajen Mustapha ya ja hannun Aysha suka shiga gida. Kayan da Sumy ta haɗa mata ya ɗauko da kuma na shi kayan kafin suka fito ya rufe gidan ya ba mai gadi keys ɗin. Napeep suka shiga don zuwa airport ya yi ta kiran number Abdallah don ya zo ya kai su airport ɗin amman bai same shi ba har ya hakura ya kira ɗan sahu. Sai da suka kisa isa aysha ta ce"Daddy ni ba zan je ba" rungume ta ya yi a jikinsa ya ce"Me ya sa ba za ki je ba princesse?" "Ni dai Daddy zan koma wajen Momy ne" da mamaki ya ce"wata Momyn?" Ta ce"Momyna mana" girgiza kai ya yi ya ce"Haba princesse ki yi hakuri kin ji idan muka dawo an kai ki wajen Momyn" sai yanzu ta saki ranta suka shiga jirgin don tarar da hajiya Rumaisa.
★Sumayya★
Ina baro wajen su Mustapha na ji wata kwalla ta zubo min ta rashin Aysha da zan yi a kusa da ni kwana biyu, sai dai kuma ta wani bangaren ina jin wani farin ciki don na san zan tsira daga masifar Mama kwana biyu. Office na nufa kai tsaye bayan na gama aikin da yake gabana na nufi gida ina shiga gida ila haɗu da Umaimah ban ko kalle ta bare kuma ta saka ran zan amsa mata na nufi hanyar bangare na sai ta ce"Juya sannu da zuwa" murmushi na yi na ce"Na'am yar uwa juya sannu da gida da zaman kashe wando" da mamaki ta ce"Sumayya ni ce mai zaman kashe wando kuma? Gyada mata kai na yi na ce"To ai babu bambanci ke da su" shiru ta yi ba ta ce komai ba ganin haka sai na ja ƙafafuna zan bar wajen.
"Sumayya ina son za mu yi magana" gyaɗa kai na yi na ce"To ina sauraren ki" kamar ba za ta ce komai ba ta ce"Ki je ki cire kayan jikinki zan zo sai mu yi maganar" "To shi kenan sai kin zo" ina gama magana na fice zuwa ɗakina. Wanka na yi kafin na yi sallar la'asar da ban samu na yi ba ina ta tunani a cikin raina wata magana ce haka Umaimah ke son mu yi da ita.
Rumaissa tun barinta gidanta hankalinta kwance yake babu wani taron kasuwanci kawai dai ta yanke shawarar barin gidanta ne don ta sha iska a rayuwarta ta duniya mutum ce ita mai don tafiye-tafiye sai dai kuma shi Mustapha babu ruwan shi da irin wannan tafiye-tafiye shi ya sa a koyaushe ta shirya za ta bar gidan ba tare da sanin kowa ba shi kuwa Mustapha ba ya iya yi mata magana saboda ba ya son bacin ranta sanadiyar son da yake yi mata kwata-kwata ba ya iya taka mata burki.
Ina gama wankan Abdallah ya shigo ɗakin ya yi murmushi ya rungume ni ya ce"Babe ya aiki?" "Alhamdulilah Qalbi ya ka yini?" "Lafiya qlau ina princesse Aysha ?" Ido na zaro na ce"Ban fahimta ba, ba cewa kuka yi na kaita gidan ubanta ba? To na kai ta"dafe goshinsa ya yi ya ce"Kai kar ki ce min haka ki ka kaiwa Mustapha ita? To me ki ka ce mishi?" Zare jikina na yi daga riƙon da ya yi min na ce"Abin da ku ka ce na yi shi na yi" zama ya yi a bakin gado ya ce"ya Salam wane irin rashin hankali ki ka aika haka Babe?" Ɗage kafaɗa ta ɗaya na yi na ce"ko ma dai wane irin rashin hankali ne abin da ku ka ce na yi shi na yi" daga nan na nufi wajen dressing mirror na shiga shafa mai sai ya ce"Babe me ki ka ce da Mustapha?" Ya yi maganar cikin ɓacin rai na ce"Ka kira shi ka tambaye shi tunda dai ka na da numbersa" haushi ne ya mamaye Misira zuciya da kuma fargaba kar a ce Sumayya ta sanar da Mustapha abin da suka ce shi da Mama akan zaman Aysha a gidan. Wayarsa ya ɗauka ya kira number Mustapha sai dai kuma ba ta shiga sai kuwa ya ƙara shiga tashin hankali marar misali ya ce"Babe kin ga abin da ki ka ka mana ko?"cikin halin ko in kula na ce"Babu abin da na ja muku illa abin da ku ka ce na yi biyayya kaɗai na yi muku kamar yadda ku ka bukata" ina gama magana ya nufi hanyar fita ya ce"Wallahi Babe sai na ɗauki mataki akan wannan abin da ki ka yi yau" yana kaiwa nan ya buɗe kofar ya fice tare da buga ta da karfi. Ni ma ci gaba na yi da abin da yake gabana
Ina gama sa kaya na zauna a bakin gado na ɗauki wayata na kira Ummi bugu biyu ta ɗaga na ce"Assalama aleikum ya Ummi" amsa min ta yi na ce"Ummi barka da gida fatan ki na lafiya?" Ummi'' da ke zaune a bakin gadonta ta ce"Ina lafiya Sumayya ya gida?" Da murna na ce"Lafiya qlau Ummi" "Lafiya me yake faruwa?" Cike da mamaki na ce"Ummi me ya faru?" "Babu abin da ya faru ina tambayar ki ne ko akwai abin da kike bukata" girgiza kai na yi kamar ina gabanta na ce"A a Ummi'' babu komai" "To sai an jima ki gaida mutanen gidan" kafin na yi magana ta katse wayar bin wayar na yi da kallo idanuna suna ciko wa da kwalla wannan wata irin rayuwa ce Ni Sumayya da wata Muryar zan yi magana na sanar da mahaifiyata ba ni da laifi ni ɗin ban aika ta wani laifi ba, sai dai kuma wannan gaskiyar ta yi min nisa faɗarta kamar ciro wuƙar yanka naman jikina ce. Na daɗe a zaune a wajen cike da zulumin da kuma mafarkin ranar da mahaifiyata za ta dauke ni a mutum ta bar kallona da da idon aibu
Tashi na yi na sauka ƙasa sai yanzu muka haɗu da Mama na ce"Mama ina yini?" "Lafiya qlau mai sunan mayu ya aiki?" Mamaki ne ya kama ni na ce"Lafiya qlau Mama" murmushi ta yi ta ce"Yauwa mai sunan Mayu dama ina son ganin ki akwai wata yar bukata gare ni" ɗago kaina na yi na kalle ta kuma na mayar da su ƙasa na ci gaba da kallon yatsun kafata sai ta ci gaba da cewa"An yi min haihuwa ne kuma ba ni da abin da zan bayar sannan kuma na tambayi Abdallah ya ce min sai dai na jira karshen wata kuma Ni gaskiya ba zan iya ba" murmushin takaici don da ma na san wannan magana da wannan doguwar gaisuwar ba a banza ba Mama take yi min ita daƙyar na fi ƙarfin kwanyata na fito daga duniyar tunani na ce"Mama me kike bukata?" Washe haƙora ta yi ta ce"Yau ina son turmin atanfa guda biyu da kuma yan kuɗin da zan hau napep da kuma wanda zan bayar na biki" shiru na yi ina nazarin mene ne Mama take son maida ni a gidan nan amman sai ta ce"Ko ba zan samu ba?" Girgiza kai na yi na ce"A a Mama za ki samu" "Yaushe za ki ba ni?" Ikon Allah kenan har lokacin da zan bayar ma sai na faɗa sai na ce"Idan sallah ya kai mu gobe ina dawowa daga office zan kawo miki" sai yanzu ta kuma sakin fuskarta ta ce"To mai sunan mayu Allah ya kai mu gobe lafiya" da amine na amsa kafin na wuce zuwa kitchen.
Sai ga Umaimah ta shigo kitcten ɗin ta ce"Na so zuwa shashenku sai na ga Abdallah ya shigo sai na hakura" ban juyo na kalle ta ba sai na ce"Ai da kin zo ma babu damuwa" "A a gara dai da na yi hakuri sai kin sauko yanzu ai zan iya sanar da ke" gyaɗa kai na yi 'a ce"Eh za ki iya sanar da ni" dan sosa kai ta fara alamar tana jin nauyin maganar amman kuma ya zama dole sai ta furta maganar sai ta ce"Ba ni da lafiya ne kuma kin san halin da muke ciki daga Ni har Hisham, to idan ba za ki damu ba ina son Aron wasu ƴan kudi domin zuwa asibiti" da kallo na bita sai yanzu na lura da sak irin yadda Mama ta yi tambayar nata kudin ita ma ta wannan hanyar ta biyo sai na ce"Allah ya ba ki lafiya idan Allah ya kai mu gobe ki shirya sai ki je asibitin zan kawo Miki kudin idan na koma daki" godiya ta min kafin ta bar kitchen ɗin Ni kuma na bi ta da idanu.
*Cmnts nd share*
[20/12 à 21:24] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780416252
🔥 KARSHEN FREE PAGE🔥
Only 300 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuma 300f ta wannan number +22780416252
*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*
*Page 15*
Bayan na gama girki na nufi ɗakina ina ta tunanin wannan bakon lamari da su Mama suka ɓulo da shi su na shirin maida ni saniyar tatsa sun ajiye banki a gida. Jakata na buɗe na ciro da yan jika goma guda biyu daidai zan fito daga ɗakin muka haɗu da Abdallah ya ce"Babe ina za ko je da kudi a hannu haka" na yi niyyar tafiya ba tare da na ce mishi komai ba ya kuma cewa"Babe magana nake yi miki' kamar ba na so na ce"Zan kai wa Umaimah kuɗi ne" "kuɗin me za ki kai mata?" Murmushin takaici na yi na ce"Ba ta da lafiya ne shi ya sa zan ba ta kudin zuwa asibiti" wani irin kallo ya yi min ya ce"Ke ce Hisham ba?" "Ka fi ni sanin ba ni ba ce Hisham amman ko ba komai ka san sarai Hisham ba shi da aikin yi bare kuma ya bada kuɗin da za