ce"Ko ke fa yarinyar kirki" wanka na gama mata na shirya ta na bata abinci ta ci kafin na ja hannunta muka sauko ƙasa don na dauki aniyar ba zan zauna a gidan ba don na yi musu tunda dai ba baiwa ba ce ni ɗin.
Ina saukowa kasa wannan ya tabbatar min da har yanzu Abdallah bai bar gidan ba amman ban damu ba na saka Aysha a mota na yi ma motar key muka bar gidan.
Abdallah ko da ya gama breakfast ɗinsa ya shiga dakin Sumayya amman bai tarar da ita ba da mamaki ya fara tunanin to ina ta je. Bai tsaya wani tunani ba ya nufi office a parking Space ya hangi motar Sumayya tunani ya fara kenan ba ta bi umarnin mahaifiyarsa ba ta saka ƙafa ta bar gidan tabbas sai ya ɗauki mataki akan Sumayya don ba zai yarda da wannan halayyar ta raini da take don tsirowa ba musamman zuwa ga mahaifiyarsa. Kwafa ya yi tare da shige wa cikin Company ya nufi office ɗinsa kai tsaye.
Da yamma ina gama aikina sai da na biya wani supermarket na yi wa Aysha siyayar kayan sawa da kuma biscuit da chocolat. A hanya sai surutu take tana ta faman kiciniyar buɗe ledar na ce"Princesse don Allah ki yi hakuri da buɗe ledar nan sai mun je gida" "Na ajiye Momy" ta faɗa kafin ta daina taɓa ledar. Ina isa gidan na yi parking na fito da ledar kafin na kama hannunta muka nufi cikin gida.
Mama Sa'a da tun safe bayan ta gama breakfast take jiran saukowar Sumayya amman shiru har ta gaji da jiran gawon shanu ta kira Rumana ta ce"Ke Rumanatu je ki kira min Sumayya" da mamaki Rumana take kallon Mama ta ce"Wata Sumayyar bayan tun ɗazu ta tafi office, ina ta jikin window ɗakina na hango ta" "kan bala'i wallahi wannan yarinya ta yi mugun raina min wayo, idan ba rainin wayo ba jiya sai da na ce ta tsaya ta yi shara amman sam ta ƙi Allah sai na ɗauki mataki akan wannan yarinyar. Idan ba jaraba irin ta Abdallah ya sawake ma wannan juyar mana ko mun huta amman kullum abin ƙara gaba yake na yi masifar na yi nasihar na yi makircin amman har yanzu ina ci gaba da bulayi bara a kufe" ita dai Rumana shiru ta yi tana ci gaba da zuba wa Mama ido da kunne don saurarenta.
"Je ki kira Jiddah ku gyara musu ɗakin kafin su iso" wani kallon mamaki take bin Mama da shi ta ce"Wa wai ni ? Wallahi ba zan yi ba a saka masu aiki ko kuwa jiddah idan ta ga za ta iya sai ta yi ɗakin da a shekara ɗaya ma ba a buɗe shi ba shi ne za ki ce wai mu share" tana kaiwa nan ta fice daga falon. Baki Mama ta saki tana kallon Rumana don dama ta san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, ya lafiyar kura bare tana zawo a banza ma Rumana ta yi ma mutum rashin kunya bare kuma an saka ta aiki. Dole uwar na ƙi Mama ta kira mai aiki ta saka ta aikin gyaran ɗakin da babban ɗanta zai zauna da matarsa.
Zama ta yi tana faman jiran dawowar Sumayya don ta sauke mata abin da yake cikinta don ba za ta dauki wannan sabon salon iskanci da Sumayyar ta tsiro da shi ba.
*Cmnts nd share*
[16/12 à 19:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780416252
🔥FREE PAGE🔥
NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?
Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.
*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*
*Page 11*
Ta riga ta saka a cikin ranta sai ta yi maganin Sumayya duk rashin kunyar da Rumana ta yi mata ba ta gabanta sai rashin kunyar Sumayya ce take gani. Ai dama an ce laifi tudu ne sai ka hau naka ka riƙa hango na wani.
Tana zaune a wajen tana ci gaba da saka da warwara bayan an gama share ɗakin da ta saka mai aikin gidan ta share, sai aka turo kofa Hisham ne da matarsa Umaimah suka shigo da sauri Umaimah ta karaso inda take zaune ta rungume Mama ta ce"Mama na yi kewarki sosai" murmsuhi Mama ta yi ta ce"To ai dama Umaimah sai da na faɗa wa Hisham ya dawo da ke gidan nan amman ya ƙi ai gashi yanzu kun dawo" ita ma murmushin ta yi ta ce"Yanzu kam Mama ai na dawo ko zan ci gaba da zama a kusa da ke"
Daidai Hisham ya karaso ya ce"Mama barka da safiya" zama ya yi akan capet kusa da kafar Mama ta shafa gashin kansa ta ce"Hisham sannu da kokari, wannan abu da ya faru sam ban ji daɗi ba, amman yanzu ai shi kenan ka bar musu gidansu sai ku zo ku rayu a gidan ɗan uwanka lafiya qlau babu wanda zai dame ka da ka biya haya" gyaɗa kai ya yi ya ce"Haka ne Mama mun gode sosai da wannan dama da ki ka ba mu" "haba haba ai babu zancen godiya ku ɗin ƴaƴana ai, ku tashi ku shiga daga ciki ku ɗan kimtsa" tashi suka yi suka nufi dakin da aka ware musu nan suka shiga gyara kayansu.
Umaimah tunda ta auri Hisham Mama ta dauki son duniya ta ɗaura mata, tun bayan aurensu yanzu shekara biyar amman sau uku tana haihuwa ƴaƴan su na mutuwa wannan ne ya ƙara ma Mama Sa'a soyayyar Umaimah a cikin ranta saboda yadda take jin tausayin Umaimah ɗin wannan dalilin ne ya sa wutar tsanar Sumayya ta ƙara ruruwa a zuciyar Mama Sa'a domin ita a ganinta ai gara Umaimah ko babu komai ita tana haihuwa Allah ne bai bar mata ba amman ita Sumayya ko ɗan ɓarin nan ma da mata ke yi ita bata taɓa yi ba. Ganin Umaimah ta samu fada a wajen Mama sai take cin karenta babu babbaka a cikin gidanta wani lokacin ko Hisham bai isa ya taka mata burki ba idan tana wani abin saboda da ya ce zai yi mata magana sai ta kira Mama ta sanar mata ita kuwa Mama ta rufe shi da faɗa daga karshe dai ita Umaimah za ta samu damar yin abin da ta ga dama
Mama ta daɗe a wajen a zaune har aka yi sallah ta tashi ta yi sallah ta dawo zaman jiran gawon shanun da take yi wa Sumayya. Can kuwa sai ga Sumayya ta turo kofar falon da sallama a bakinta hannunta kuma riƙe da Princesse Aysha da ledar siyayar da suka yi a super market.
★SUMAYYA★
Da sallama na shigo gidan sai na lura da Mama zaune a falo na ce"Mama ina yini?" Wani kallon mai akan ruwa ta yi min nan na fara tunanin abin da na yi mata ni kuwa magana na ji tana yi wa Aysha "Mai babban suna ina Mamanki?" Aysha ta amsa mata "Momy tana gida wajen Daddy" na ce"Aysha mu je a yi wanka ko?"
Har mun fara tafiya na tsinkayo muryar Mama tana cewa"To marar mutunci banza shasha da bata san ciwon kanta ba, a haka dai za a ƙare a rainon ƴaƴan wasu kai ba ka da naka" ban ce komai ba idan a ce ana yin sabo da mugayen maganganu ni kam da tun tuni na yi sabo da wannan cin kashin na Mama. Sai dai kuma ita zuciya ba ta da ƙashi tsoka ce, duk wannan abin da Mama take yi min na kasa kauda kai sai ta ci gaba da cewa "Tsabar isakanci irin naki da na saka ki aiki sai ki ka figi wannan kafafun naki masu kama da karas ki ka bar gidan nan ko? Wallahi ki kiyaye ni ki fita nesa da ni na faɗa miki, wannan ya zama karo na farko kuma na karshe da zan saka ki wani abu a gidan nan ki saka ƙafa ki shure shi sai na yi mugun ɓata miki rai wallahi. Ina dalilin wani aiki, aikin banza aiki wofi, kullum mutum yana saka wasu ɗangalalun kaya ya bar gida da sunan wani aiki ko. To ki yi a hankali don ina gab da hana yin wannan aiki sai dai ki zaɓa zama da Abdallah ko kuwa aikinki" shiru na yi ina nazarin amsar da zan bata amman sai na rasa abin faɗa sai na bi jikina da kallo doguwar rigar atanfa ce a jikina ta buɗe sosai har tana sharar ƙasa ga wani babban mayafi da na saka kuma a haka za a ce dangalalun kaya ne, kawai na gyaɗa kai na ja hannun Aysha muka bar falon don zuwa shashena
Ina jinta tana ci gaba da bambamin faɗanta amman ban tanka mata ba.
Ina shiga dakina Aysha ta ce"Momy ina jin yunwa" gyaɗa mata kai na yi na ce"Za ki ci indomie?" Da sauri ta girgiza min kai ta ce"A a Momy ba na so" shiru na yi ina nazarin abin da zan sama mata ta ci yanzu-yanzu saboda Allah ya sani a gajiye nake sosai. Ganin dai babu sarki sai Allah sai na ce"Bari na dauko miji madara ki sha kafin na gama girki" sai ta fara dariya har da tsalle don murna.
Cire kayan jikina na yi na saka wasu na ja hannunta muka sauka ƙasa zuwa kitchen don na haɗa dinner sai ita kuma na bata madara ko na samu sallama don da an jima za ta fara yi min kukan yunwa take ji. Muna shiga kitchen na dauko mata madara na daura ta akan kujera na shiga store don duba abin da zan girka.
Jiddah ce ta shigo kitchen idonta ya sauka akan Aysha da take shan madara har ta fara ɓata rigar da ke jikinta ta ce"Kan uba ashe ba ki da mutunci wannan yarinyar to uban waye ya baki madarar har da za ki ɓarnatar da ita" Aysha kam sai yanzu ta ɗago kai ta kalli jiddah ganin ta fara zaginta tuni har idonta ya fara kawo kwalla ta ce"Momy ce ta ba ni" hannu ta saka ta kwace cup ɗin da Sumayya ta zuba mata garin madarar a ciki ta ce"To dan uwarki ba za ki sha ba je ki gidan ubanki sai ki sha a can tunda dai wannan babu kudin uwarki a ciki" fashe wa Aysha ta yi da kuka. Daidai na bude kofar store ɗin na fito don duk abin da jiddah ke faɗa akan kunnena sai kuma na yi mugun ganin tozali da na yi da jiddah tana zungurar mata goshi.
"Jiddah lafiya me ta yi miki haka?" Na tambaye ta don jin ba'asin dalilin da ya sa ta shiga haƙƙin yarinyar da ba komai ta ce mata ba. "Kawai na ce madara ce ba za ta sha ba don ba uwarta ta siya ba" wani mamaki ne ya kama ni tunda nake a cikin gidan nan jiddah da Rumana ba su taɓa faɗa min wata magana ba ni da su kare ba zan baka ba kuma ba zan kore ka ba. Ko gaisuwa ba ta haɗa mu sai wasu ƴan maganganu masu muhimmanci kadai ke shiga tsakanin amman yau shi ne har za ta faɗa min magana ba sai na ce"Jiddah ke ki ka siye madarar da Aysh take sha?" "Ba ni na siya ba amman yayana ya siya kin ga na fi ta iko da madarar" kwace cup ɗin na yi daga hannunta na ce"Idan yayanki ya zo ki turo shi ya kwace madarar daga hannunta wannan na san mai iko da abin ne ba ke ba karan kaɗa mita kawai" dariya ta yi ta ce"To juya ma ta fara magana, don Allah ki ji da abin da ya dame ki na rashin haihuwarki zai fi miki" da ido na bita har ta bar kitchen ɗin ban so na tanka mata ba amman abin nata ya wuce makaɗi da rawa wajen da Aysha ke zaune na je na shiga share mata hawaye na ce"Ki yi hakuri princesse ki rabu da jiddah sha madararki kin ji" girgiza min kai ta yi ta ce"Ni ice cream zan sha" dare goshina na yi don kaina bala'in ciwo yake min na ce"To ki sha madarar idan muka gama cin abinci dare zan siyo miki ice cream ɗin" gyaɗa kai ta yi kafin ta karbi cup ɗin ta shiga sha ni kuma na fara kiciniyar girkin abincin dare.
"Sumayya! Sumayya! Sumayya ashe ba ki da mutuncin ban taɓa sani ba sai yau, to uban me Jiddah ta yi miki da za ki dake ta ke ki ka haifar min ita ne?" Da mamaki na kalli Mama da yanzu ta shigo kitchen ɗin sai masifa take kamar ta ari baki na ce"Mama me aka ce na yi kuma?" "Au, ba ki ma san abin da ki ka yi ba kenan" girgiza kai na yi alamar ban sani ba ta ce"To uban wane ne ya daki jidddah?" "Ni kam ban sani ba don ban dake ta ba" "To karya za ta yi miki ne? Na ce karya za ta yi miki?"
Abdallah da tun shigowar Mama yake tsaye a bakin kofar kitchen ɗin duk abin da ya faru akan idonsa amman bai yi magana ba sai yanzu ya ce"Mama rabu da ita zan yi mata magana" juyo wa Mama ta yi ta kalle shi kafin ta ce"To dai ka gani yanzu isakanci matarka har wanda ku ka fito ciki ɗaya da su yi wa take yi" kafin ta fice daga kitchen. Wajen Aysha ya karasa ya ce"Princesse ki bani madarar mana" ba ta yi musu ba ta miƙa mishi cup ɗin ya yi mamaki don ya san sarai Aysha ba ta kyautar madara sai ya ce"Yau kuma ƴan kyautar ne kenan?" Girgiza kai ta yi ta ce"Ni ice cream nake so" "to ki gama shan madara sai mu je mu siyo" nan ma girgiza kai ta yi ta ce"Ni dai yanzu nake so" sai lokacin ne ya kalle ni ya ce"Ki canza mata kaya za mu fita" daga nan ya fice daga kitchen ɗin. Ni kuma mai aiki na kira na ce ta duba min tunkuyar da na daura sai na je na canza wa Aysha kaya
Ina shiga falon na kai ta ɗakina kafin na shiga dakin Abdallah na ce"Qalbi sannu da zuwa, ya aikin?" Bai ko kalle ni bare kuma na saka ran zai amsa min sai na kuma cewa"Qalbi lafiya kuwa?" Wani kallo ya watso min da idanunsa wanda nake hango tsantsar bacin rai a cikinsu sai da gabana ya fadi don a wannan karon ban san abin da na yi ba, murya na rawa na ce"Qalbi magana nake" sai yanzu ya shirya yi min magana ya ce"Zauna" guri na samu a kusa da shi na zauna tare da zuba mishi idanu ina jiran jin abin da ni Sumayya na aikata.
"Babe mene ne matsalarki ke kam? Jiya Mama ta saka ki aiki ba ki yi sai ki ka share umarninta ki ka fice daga gidan nan ko?" An zo wajen yanzu kam sai ya ci gaba da cewa"Na zuba miki ido don ganin gudun ruwanki amman yau ma kuma sai na tarar da ke kin kuma ɓata mata rai, Babe ba na son wannan sabon halin da ki ka tsira. Mahaifiyata tamkar mahaifiyarki take don haka dole ne ki yi mata biyayya kamar yadda za ki yi min kuma ki yi ma mahaifiyarki" gyaɗa kai na yi na ce"Qalbi na fahimta sosai kuma in sha Allah za a gyara, amman maganar ɗazu guguwar fahimta ce ka yi wa lamarin don ni sam ban daki Jiddah ba" hannu ya ɗaga ya ce"Ya isa Babe, Mama ce ta yi ƙarya ko kuwa ya maganar take? Wai me kike son zama ne yanzu?" Buɗe bakina na yi da niyyar yin magana sai dai ya yi saurin ce min tashi ki je ki shirya Aysha za mu tafi siyan ice cream"
Tashi na yi kamar yadda ya bukata na bar dakin. Kaya na ciro da Aysha na shirya ta kafin na ce"Je ki Uncle yana dakinsa sai ku tafi" bye bye ta yi min kafin ta fice daga ɗakin, zama na yi a bakin gadona na fashe da kukan baƙin cikin da yake cin raina
*Cmnts nd share*
[17/12 à 22:46] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW
*DA WATA KUSAN...*
NA
Zouley Sabitou (Émilia)
Daga marubuciyar *KUSKURE*
☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️
(Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation)
GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.
+22780416252
🔥FREE PAGE🔥
NA KUSA GAMA FREE PAGE HAJIYA ME KIKE JIRA BA KI BIYA KUDIN KARATUNKI BA?
Only 500 za ki biya ta wannan account ɗin Faiza abubakar 9030283375 opay
Yan Niger kuwa dépôt myNita 500f a wannan number 93885676 ko kuma carte Airtel ko orange.
*Duk wadda ta biya kuɗin karatunta ta turo da évidence ta wannan number +22780416252*
*Page 12*
Sai da na yi kukana mai isata kafin na share hawayena na sauka ƙasa don ci gaba da girkina ko da na sauko ƙasa babu kowa shiru kamar an yi ruwa an ɗauke daidai zan shiga kitchen ɗin muka yi kicibis da Umaimah na ce "Anty Umaimah sannu da zuwa" wani banza kallo ta jefo min kafin ta ce"Juya ashe ki na gidan?" Tamkar saukar wata guduma haka Muryarta ta daki kunnena da kuma zaginta a gare ni ban ce komai ba sai na matsa mata daga hanya sai da ta fice daga kitchen kafin ni kuma na shiga.
Abdallah kuwa bayan sun fita daga gidan tare da Ayhsa parking Space ya nufa inda ya ɗauki motarsa ya buɗe wa Tasha gidan gaba kafin ya shiga shi ma. Sai da ya fara driving sai Tasha ta ce"Uncle ka na son na faɗa maka wani abu?" Gyaɗa kai ya yi ya ce"Princesse ba ni labari abin da ya faru" murmsuhi ta yi kafin kuma cike da yarinta ta ce"Ɗazu anty Jiddah ya karɓe min madarata da Momy ta ba ni kuma ta ce ba zan sha ba tunda dai ba uwata ba ta siya" wani ras gabansa ya fadi daƙyar ya iya daure wa ya ce"Ita anty jiddah ta ce haka?" "Kwarai kuwa daddy har da haka ta yi min" ta faɗa tana zungurin kanta da yatsarta "kuma ta ce wai ai ba Momy ba ta siya yayanta ne siye madarar" ransa ya kai kololuwa wajen ɓaci kenan dai wannan dalilin ne ya saka Mama zuwa wajen Sumayya tana yi mata faɗa kamar ta ari baki. Ya ce"ki yi hakuri princesse ba za ta ƙara yi miki haka ba ita jiddah" gyaɗa kai Aysha ta yi ta ce"To uncle wane ne yayan anty jiddah?" Wani iri ya ji tambayar kamar wanda wani babba yake yi jera mishi wasu tambayoyi sai dai ya ce"Ni ne yayanta princesse" sai ta ce"Uncle to ka bari na sha madara tunda kai ka siye ta ka ji" da sauri ya gyada kai ya ce"To princesse idan ki na so ma ki shanye duka kuma yanzu ma zan siyo miki wata" ihun murna ta fara. Kafin suka yi parking a bakin shagon da ake siyar da ice cream suka shiga, tunani ne fal ransa sai dai kuma duk hankalinsa ya bi ya tashi domin gani yake yi sam bai yi wa Sumayya adalci ba tunda dai bai barta ba har ta kare kanta daga zargin da ya kafa mata ba amman kuma yana son mahaifiyarsa fiye da duk tunanin mai tunani shi ya sa idan dai akan ne ba ya tsayawa wani dogon nazari zai hukunta duk wanda ya shiga gonarta.
Sai da suka biya wani katoton mall ya siya mata madara kafin suka nufi gida.
Isar su gida ke da wuya aysha ta kwasa a guje sai cikin gida duk kiran da Mama take yi mata ba ta bi ta kansa ba sai da ta isa har dakin Sumayya.
Ina zaune a bakin gado don ni ma yanzu na shigo dakin sai ga Aysha ta shigo da gudu tana ta murna na ce"Princesse mene ne ya zo garin wannan uwar murna haka?"Da murna ta ce"Momy kalli uncle ya siya min" da sauri na amshi ledar da ke hannunta na buɗe sai na ce"Princesse cewa uncle ki ka yi ya siya miki?" Ta girgiza kai ta ce"Momy na faɗa mishi abin da anty Jiddah ta yi min ne" girgiza kai na yi cike da alhini na ce"to zauna ki sha ice cream ɗin" tana zama ni kuwa na tashi na nufi falo daidai shigowar Abdallah
Yana karasowa na ce"Qalbi sannu da zuwa" sai da ya zaune kafin ya ce"Yauwa Babe ya gidan?" Da lafiya qlau na amsa sai ya ce Babe ɗazu me ya sa ba ki faɗa min abin da ya faru tsakaninku da Jiddah har ta daki Aysha" girgiza kai na yi na ce"Ai ba ka bukaci sanin abin da ya faru ba saboda ka ce na rufe bakina" shiru ya yi kamar ruwa ya cinye shi ya ce"Ina mai baki hakuri akan abin da na yi" haushin shi ma nake ji yanzu kam amman sai na daure na ce"babu komai ai ya wuce" tashi ya yi ya sauka a ƙasa ya shiga kwala kiran Jiddah. Tana fito wa ya zuba mata ido tare da cewa"Uban me Aysha ta yi miki har ki ka dakar musu ƴa" Mama da yanzu ta fito daga dakinta ta yi saurin amshe zancen "To shanyaye an zana maka ƙarya da gaskiya ka hau kai ka zauna ko tsabar rashin tunani" cewa ya yi "Mama babu wanda ya zana min karya da gaskiya sai dai iya tsagwaran gaskiyar aka faɗa min" ido Mama ta zaro ta ce"Sakaran banza ni wannan duk ihun da kake yi fa akan mace ne, ina dalili kira wancan matar taka ta mayar da yarinyar gidan ubanta ai ba dole ba ne ko zaman nata a nan gidan" Baba ne yanzu ya shigo gidan ya ce"Ke Sa'a ba ki da mutunci ashe to yarinyar da ake magana a kanta ko babu Sumayya a nan gidan ta kai matsayin da zai riƙe ta saboda ƴarsa ce halak malak"
"Tab ƴar Mustapha dai to ai Abdallah juya ne kamar matarsa" Umaimah da fitowar ta kenan daga ɗaki ta faɗa tana mai fashe wa da dariya ganin wani irin kallo da Mama ta yi mata sai ta y saurin cewa"Mama ina nufin ai shi Abdallah ba shi da ƴa kin ga kuwa ai wannan ba za a ce tasa ba ce yarinya ta koma gidan ubanta zai fi" wata ajiyar zuciya Mama ta sauke kafin kuma ta ci gaba da cewa" gobe idan Allah ya kai mu kar a maido yarinyar nan gidan nan ta tafi gidansu" tana gama magana ta bar falon ba to ko bi ta kan abin da baba ke faɗa ba.
Ita kuwa jiddah tuni ta sha jinin jikinta don ta san sarai mai raba ta da Abdallah a gidan nan sai ya dage juyo wa ya yi cike da masifa kanta domin fara yi mata balbalin bala'i. Tun farkon dambarwar su har zuwa yanzu Sumayya na tsaye daga gefen corridor tana kallon su sai yanzu ta fito daga maɓoyarta.
A hankali na karasa tsakiyar falon na ce"Qalbi ka rabu da ita gobe idan Allah ya kai mu zan mayar da Aysha gidansu" ina gama magana ba juya na bar falon ban tsaye sauraren abin da Abdallah zai ce min ba.
Ina shiga falo na yi zaman jugum ina tunanin ta ina zan fara kiran Mustapha har na ce ya zo ya ɗauki ƴarsa bayan kuma ina da tabbacin Rumy ba ta dawo daga yawonta, na shiga tashin hankali don wannan shi ake cewa ga mutuwar uwa ga soyen nama. Ga masifar mutane gidan nan akan zaman aysha